Tinubu Ya Sauka daga Shugabancin ECOWAS, an Faɗi Wanda Ya Maye Gurbinsa
- Shugaban Sierra Leone, Julius Bio, ya zama sabon shugaban ECOWAS bayan ya karɓi kujerar daga hannun Bola Tinubu a taron da aka yi a Abuja
- Bio ya ce zai maida hankali kan dawo da tsarin mulki, haɗin gwiwar tsaro da kuma bunƙasa haɗin tattalin arzikin yankin
- Ya yabawa Tinubu saboda “kyakkyawan shugabanci” da jajircewa wajen samun zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arzikin yankin ECOWAS
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban kasar Sierra Leone, Julius Bio, ya zama sabon shugaban Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS).
Bio ya gaji Shugaba Bola Tinubu, wanda ya shugabanci kungiyar ta yankin Afrika ta Yamma na tsawon shekaru biyu da suka wuce.

Asali: Twitter
An maye gurbin Tinubu a shugabancin ECOWAS
Hadimin Bola Tinubu a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Lahadi 22 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasar Sierra Leone ya karɓi shugabancin daga hannun Tinubu a ranar Lahadi yayin zaman taron shekara ta 67 da aka gudanar a Abuja.
Kafin zaɓen, akwai jita-jita cewa shugaban Senegal, Bassirou Faye, ne zai karɓi shugabancin kungiyar da ke fama da matsaloli.
Bio ya yi alkawarin mayar da hankali wajen dawo da tsarin mulki da kuma zurfafa dimokuradiyya a yankin da ke fama da rikice-rikice.
Haka kuma, ya bayyana cewa za a dawo da haɗin gwiwar tsaro, a ƙarfafa haɗin tattalin arziki, da kuma gina sahihancin cibiyoyin kungiyar.

Asali: Facebook
Kalubalen da Tinubu ya fuskanta a shugabancinsa
An zaɓi Tinubu a karon farko a Guinea-Bissau a ranar 9 ga Yulin 2023, kasa da wata biyu kenan bayan an rantsar da shi a mulki.
Har ila yau, an sake zaɓensa a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS bayan shekara guda watau a shekarar 2024 a birnin Abuja.
Zaman shugabancinsa ya fuskanci ƙalubale na maido da dimokuradiyya saboda kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga kungiyar bayan juyin mulki.
ECOWAS: Shugaba Bio ya yabawa Bola Tinubu
Shugaba Bio ya yabawa Tinubu saboda “kyakkyawan shugabanci” da “jajircewarsa wajen tattaunawar yanki, farfaɗo da tattalin arziki da gina zaman lafiya.
A jawabinsa na karshe a matsayin shugaban ECOWAS, Tinubu ya roƙi kasashen guda uku da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso da suka fice daga kungiyar da su dawo ciki
Tinubu ya yi Allah wadai da kisan matafiya
Kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan kisan da aka yi wa ƴan ɗaurin aure a Plateau da ke Arewacin Najeriya.
Tinubu ya bayyana kisan gillar a matsayin abin ƙyama wanda ba za a amince da shi ba ko kaɗan iska ya ce dole za a ɗauki mataki kan wadanda suka aikata hakan.
Shugaban ƙasar ya umarci hukumomin da su tabbatar da cewa sun zaƙulo masu hannu a harin da aka kai kan matafiyan da suka taso daga Kaduna a Arewa maso Yamma.
Asali: Legit.ng