Sule Lamido Ya Fito da Manyan Zarge Zarge kan Tinubu game da 12 ga Yuni
- Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya caccaki jawabin Shugaba Bola Tinubu na ranar Dimokuraɗiyya, yana zarginsa da ƙoƙarin ɓata tarihin ƙasar
- Lamido ya ce Tinubu yana kafa salon mulkin kama-karya ta hanyar tattara iko da daukar kansa matsayin sarki cikin ƙasar da ake ikirarin dimokuraɗiyya
- Ya kuma soki bayar da lambobin girmamawa da kuma nadin mukamai da ya ce bisa siyasa da son rai aka yi su, yana cewa lamarin ya kaskantar da dimokuraɗiyya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin ɓata tarihin gwagwarmayar dimokuraɗiyya ta ranar 12 ga Yuni.
Lamido ya bayyana jawabin shugaban ƙasa da aka gabatar a ranar Dimokuraɗiyya a matsayin yunkurin karkatar da tarihi.

Asali: Twitter
Rahoton Arise News ya nuna cewa Lamido ya ce Tinubu yana kokarin ƙirƙirar sabon tarihin 12 ga Yuni
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule Lamido ya ce alamu sun nuna hakan musamman lokacin da ya haɗa sunan kansa da Sanata Ameh Ebute cikin jerin gwarazan gwagwarmayar ranar 12 ga Yuni.
Tsohon gwamnan ya ce Ebute dai ya zama shugaban majalisa ne bayan da soja suka sauke Sanata Iyorchia Ayu, wanda ya bijire wa shirin mulkin kama-karya.
Sule Lamido ya zargi Tinubu da kama karya
Sule ya bayyana damuwa kan yadda Tinubu ke tattara iko a hannunsa kamar yadda sarakunan da suka gabata ke yi, yana mai cewa hakan na iya jefa Najeriya cikin mulkin danniya.
Ya ce:
“Yanzu muna ganin duk abin da aka gina ana sanya masa sunan mutum daya ne — Tinubu. Wannan ba dimokuraɗiyya ba ce.”
Ya ci gaba da cewa:
“Wannan ƙasar fa ba mallakar wani mutum ɗaya ba ce. Lokacin da kake ɗaukar kanka kamar Allah kuma ka kewaye kanka da ‘yan amshin shata, zaka ƙare da kunya ne.”
Sule ya soki matakin Tinubu a Ribas
Dangane da rikicin siyasa da ke gudana a Ribas, Lamido ya soki matakin Shugaba Tinubu na nada gwamnan rikon kwarya, yana mai cewa hakan saba wa kundin tsarin mulki ne.
Ya ce:
“Ko a lokacin da aka ayyana dokar ta-baci, kundin tsarin mulki bai ba shugaban ƙasa ikon kafa gwamnati a jiha ba. Wannan hari ne kan dimokuraɗiyya.”

Asali: Instagram
Tsohon 'dan siyasar ya goyi bayan kalaman Sanata Seriake Dickson da ya soki tsarin shugabancin Tinubu, yana mai cewa Dickson ya faɗi gaskiya a kan kokarin murkushe dimokuraɗiyya.
Maganar Sule Lamido kan girmama mutane
Tsohon gwamnan ya kuma zargi gwamnati da mayar da tsarin bayar da lambobin girmamawa matsayin kayan siyasa, yana cewa:
“Me ya sa ake bai wa waɗanda suka ci amanar ƙasa lambar girma? A da ana ba da lambobin ne bisa cancanta. Yanzu kuwa son rai da biyayya ake dubawa.”
Tinubu zai kafa 'yan sandan jihohi?
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne a wani taron kan sauya tsarin mulki da aka shirya a Abuja da ministan tsaro ya wakilce shi.
Shugaban kasar ya ce ya zama dole a samar da 'yan sanda a jihohi lura da yadda ake fama da matsalar tsaro a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng