'Ana Zaluntar 'Yan Najeriya': An Ji Farashin da Ya Kamata a Rika Sayar da Fetur

'Ana Zaluntar 'Yan Najeriya': An Ji Farashin da Ya Kamata a Rika Sayar da Fetur

  • PENGASSAN ta zargi dillalan mai da sayar da fetur da tsada tana mai cewa bai kamata 'yan Najeriya su sayi litar fetur sama da N750 ba
  • Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce danyen mai ya fadi daga $80 zuwa $60, amma 'yan kasuwa sun ki rage farashin a gidajen mai
  • Ya dora alhakin tsadar mai kan NMDPRA yana mai cewa hukumar ta gaza sa ido yadda ya kamata kan yadda 'yan kasuwa ke tatsar mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta zargi 'yan kasuwar mai da zaluntar 'yan Najeriya ta hanyar yin tsadar fetur a gidajen mai.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, shugaban PENGASSAN na kasa, Festus Osifo, ya ce 'yan kasuwa na sayar da litar fetur a kan N900 duk da cewa mai ya fadi kasuwar duniya.

PENGASSAN ta ce N700 zuwa N750 ya kamata 'yan Najeriya su rika sayen litar fetur.
'Yan Najeriya suna layin sayen man fetur a daya daga cikin gidajen mai mallakin NNPCL. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

PENGASSAN ta magantu kan tsadar man fetur

Festus Osifo, ya nuni da cewa farashin da ake sayar da gangar danyen mai a duniya ya fadi daga $8 zuwa $60, amma 'yan kasuwar Najeriya sun ki rage farashi, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osifo ya dora laifin irin wannan tsawwala farashin da gidajen mai suke yi a kan hukumar kula da man fetur ta NMDPRA, yana mai cewa ta gaza sa ido kan yadda ake sayar da man.

Yayin da yake kira ga gwamnati da ta dauki tsaurara matakai, shugaban PENGASSAN ya ce:

"Bai kamata hukumar NMDPRA ta zura idanu tana kallon 'yan kasuwa suna tatsar 'yan kasa, alhalin an ce ana kiyaye farashin da ake sayar da man."

Farashin da ya kamata a sayar da fetur

Ya bayyana cewa ana kayyade farashin litar man fetur ne a yanzu ta hanyar auna farashin da ake sayar da danyen mai da farashin canjin kudi, wanda kusan ke samar da kaso 80% na kudin.

"Idan ya zamana cewa ana sayar da gangar danyen mai a kan $60 kuma akwai daidaito a canjin kudi, to bai kamata a sayar da fetur sama da N750 ba. Ya kamata a sayar da shi tsakanin N700 zuwa N750."

- Festus Osifo.

Ya kuma buga misali da ma'aunin PLATTS, wanda ake amfani da shi wajen kayyade farashi a duniya, yana mai cewa, idan aka lissafa da kyau, za a ga cewa zalunci ne idan 'yan Najeriya na sayan litar fetur kan N900.

Festus Osifo ya kuma amince cewa kowane dan kasuwa yana yin kasuwanci ne don riba, amma ya jaddada cewa bai kamata a rika neman ribar ta hanyar tatsar talaka ba.

PENGASSAN ta bukaci gwamnati ta dauki mataki don kayyade farashin da ake sayar da fetur
Shugaban kungiyar PENGASSAN na kasa, Festus Osifo yana jawabi a taron makamashi da kwadago na 2024. Hoto: PENGASSAN
Asali: Twitter

PENGASSAN ta magantu kan rufe matatar Port Harcourt

Ya bukaci hukumar NMDPRA da ta fitar da farashin da aka kayyade na sayar da fetur domin kare 'yan Najeriya daga sayen mai a farashi mai tsada.

Jaridar Tribune ta rahoto shugaban PENGASSAN yana gargadin cewa:

"Idan aka ci gaba da tatsar 'yan Najeriya, to zai zamana cewa 'yan kasar ba za su amfana daga faduwar farashin danyen mai ba, sai dai su rika shan wahala idan farashin ya karu."
Ya kuma nuna matukar damuwa kan yadda ake samun jinkiri a wajen gyara matatun man Najeriya, musamman yadda aka dade ba tare da an sake bude matatar Port Harcourt ba.
"Abin damuwa ne kwarai yadda ake ci gaba da rufe matatar mai ta Port Harcourt, duk da cewa an narka mata kudade masu yawa wajen gyara ta."

- Festus Osifo.

Mutane sun yi korafi kan farashin mai a Kaduna

A zantawarmu da wasu mazauna Kaduna, sun yi korafi kan yadda farashin fetur din ya ki sauka duk da cewa suna jin labarin matatar Dangote na sauke farashi.

Hassan Baban Nur, wanda ya ce sun samu matsalar na'urar da ke ba su wutar lantarki, ya ce yana kashe kudi masu yawa wajen sanya mai a janareta.

"Taransifomar anguwarmu ta lalace, kusan kwana takwas kenan ba mu da wuta. Cajin waya ya koma N200, ga matsalar rashin ruwa, dole sai na sayo fetur na tayar da janareta don canji da samun ruwa.
"A unguwarmu yanzu, man N1200 bai kai rabin galan ba. Galan kuwa ta kai N3000. Muna da tazara da gidan mai, dole take sa mu sayi man wajen 'yan bunburutu."

Wani direban adaidaita sahu, Kabiru Emole, ya ce yana samun kusan N25,000 zuwa N30000 idan ya yi aikin kwana biyu.

"To amma ai wannan kudin kusan rabi a mai suke kare wa. Ga kudin 'balance' da nake biya kullum. To za ka ga ni bai fi na tsira da N10,000 ba.
"Shi ya sa nake kokari na ga na gama biyan kudin keken nan, zan sayar da ita ne kawai na sayi mai amfani da gas, an fi samu da ita a kan mai fetur."

- Kabiru Emole.

Dangote zai raba fetur kyauta ga 'yan kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Alhaji Aliko Dangote zai fara raba man fetur da dizel daga ranar 15 ga watan Agusta, 2025, a faɗin Najeriya ga abokan hulɗarsa.

Rahotanni sun nuna cewa za a yi amfani da sababbin tankoki 4,000 masu amfani da iskar gas na CNG domin jigilar man fetur din kyauta.

An ruwaito cewa Dangote ya ɗauki wannan mataki ne da fatan zai taimaka wajen rage farashin man fetur da kuma farashin kayayyaki a kasuwanni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.