IBB @ 78: Takaitaccen tarihin Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Ibrahim Badamasi Babangida wanda a ka fi sani da IBB a Najeriya ya mulki kasar nan tsakanin 1985 zuwa 1993 a lokacin soji, ya cika shekaru 78 da haihuwa a Duniya a karshen makon nan.
Mun kawo takaitaccen tarihin tsohon shugaban kasar wanda ya kifar da gwamnatin Buhari a 1985.
1. Ibrhaim Babangida ya na da hannu a kusan duka juyin mulkin da a ka yi a Najeriya daga na Yulin 1966. Ya na cikin wadanda su ka kifar da gwamnati a 1976 da kuma juyin mulkin shugaba Buhari har ya samu zama shugaban kasa.
2. A Satumban 1969 Ibrahim Babangida ya auri Mai dakinsa Maryam Babangida. Maryam Babangida ta zama Uwargidar Najeriya tsakanin Disamban 1985 da Agustan 1993. Mai dakin tsohon shugaban ta rasu ne a shekarar 2009.
3. Janar Ibrahim Babangida da Mohammed Magoro su na cikin Daliban farko na Kwalejin sojoji na NMTC. Daga bayan manyan Sojojin sun je kasar Indiya sun yi karatu. Daga baya IBB ya zama shugaban kasa bayan ya yi juyin-mulki.
KU KARANTA: Buhari ya aikawa Babangida wasika bayan zagayowar ranar haihuwarsa
4. IBB ya na cikin wanda su ka rusa juyin mulkin da Kanal Buka Suka Dimka ya shirya a 1976. Janar Babangida ya takawa Janar Mamman Vatsa da Gideon Orkar burki a lokacin da su ka nemi su hambarar da gwamnatinsa a Legas.
5. Babangida ya yi kokarin dawowa da tsarin farar hula a 1989 inda a kirkiri jam’iyyun siyasa. An yi dace an kafa majalisu da gwamnonin jihohi. Amma ba a ci nasarar kammala zaben shugaban kasa ba inda ya rusa zaben MKO Abiola.
6. A cikin shekarar 1989, Sarauniya Elizabeth II ta Ingila ta karrama shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida da sandar girman Grand Cross of the Bath (GCB). Bayan shekaru hudu da wannan IBB ya hakura ya ajiye mulki a Najeriya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng