Matatar Dangote Ta Sake Tausaya wa Ƴan Najeriya, Ta Rage Farashin Mai
- Matatar Dangote ta rage farashin man dizal da Naira 125 kan kowace lita, inda yanzu ake sayar da shi kan Naira 1,595
- Rage farashin ya fara aiki ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, 2026, kuma ya shafi manyan masu saye da dillalan mai
- Matakin na iya rage wa masana'antu da 'yan kasuwa kudin gudanar da ayyukansu, musamman wadanda ke amfani da dizal wajen samar da wutar lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos - Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin man dizal da Naira 125 kan kowace lita, daga Naira 1,720 zuwa Naira 1,595.
Matatar ta ce sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, 2026, kuma ya shafi manyan masu sayen mai da dillalan da ke lodin dizal kai tsaye daga matatar.

Kara karanta wannan
Sarakunan Arewa da aka taba tsigewa, kora ko sallama kafin dakatar da Sarkin Daura a 2026

Source: UGC
Rage farashin da ya kai kashi 7.27 cikin 100 na iya kawo sauki ga masana'antun da 'yan kasuwa da ke amfani da dizal wajen gudanar da ayyukansu, cewar The Nation.
A sanarwar farashin da matatar ta fitar, ta tabbatar da sabon farashin tare da bayyana cewa za ta mayar da kudaden da suka samu sakamakon rage farashin zuwa asusun kwastomominta.
Yawan dizal da ake samu a Najeriya ya karu
Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake samun karuwar wadatar dizal a kasuwannin Najeriya.
Bayanan Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Rarraba Shi (NMDPRA) sun nuna cewa yawan dizal da ake shigarwa kasuwar cikin gida ya karu da kashi 93 cikin 100 a watan Oktoba.
An samu karuwar daga lita miliyan 8.7 a kullum a watan Satumba zuwa lita miliyan 16.8 a watan Oktoba.
Rahoton ya nuna cewa shigo da dizal daga kasashen waje ya karu sosai, inda ya kai lita miliyan 6.1 a kullum daga lita miliyan 600,000 da aka samu a watan Satumba.

Kara karanta wannan
Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 24 cikin wasu 157 da za a fatattako daga kasar
Haka kuma, samar da dizal a cikin gida ya karu da kashi 32 cikin 100, inda ya kai lita miliyan 10.7 a kullum, cewar Daily Post.
Duk da karuwar wadatar man, amfani da dizal a kullum ya karu da kashi bakwai cikin 100, daga lita miliyan 14.5 a watan Satumba zuwa miliyan 15.5 a watan Oktoba.
Tarihin rage farashin dizal
Wannan ba shi ne karo na farko da matatar Dangote ta rage farashin dizal ba, domin a watan Oktoba ta sauke shi daga Naira 1,780 zuwa Naira 1,700 kan kowace lita.
Sabon matakin na iya rage kudaden da masana'antu, masu harkar sufuri da sauran 'yan kasuwa ke kashewa wajen gudanar da ayyukansu.
Sai dai tasirin rage farashin zai dogara ne da yadda dillalan mai za su mayar da sabon farashin zuwa wuraren ajiyar mai da gidajen sayar da man fetur.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng