Atiku Ya Taso Tinubu da NNPCL gaba a Yi Bayanin inda Naira tiriliyan 1.4 Ya Maƙale

Atiku Ya Taso Tinubu da NNPCL gaba a Yi Bayanin inda Naira tiriliyan 1.4 Ya Maƙale

  • Atiku Abubakar ya buƙaci Bola Tinubu da NNPCL su yi bayani game da raguwar Naira tiriliyan 1.44 a kuɗin shigar Najeriya
  • ‘Dan takaran shugaban ƙasar na ADC ya ce abin da aka yi tsammanin samu daga mai a farkon watannin 2026 ba su fito ba
  • Atiku ya ce gwamnati na ƙara wa 'yan Najeriya wahalar rayuwa ta hanyar tsadar fetur, alhali ta gaza samun kuɗin da aka ci buri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya sake bi ta kan shugaban ƙasa.

Alhaji Atiku Abubakar ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) da su yi bayani dangane da zargin ɓacewar kuɗi.

Atiku
Atiku Abubakar da sauran 'yan ADC ana kamfe a Kogi Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya tado zancen bacewar N1.44tr

Jaridar Leadership ta rahoto cewa babban ‘dan adawan yana zargin cewa Naira tiriliyan 1.44 sun yi ƙafa daga cikin kuɗin shigar Najeriya na mai.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Atiku ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da tawagar yaƙin neman zaɓensa ta fitar ranar Laraba.

Ya buƙaci Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ba ta iya samun komai ba illa Naira tiriliyan 7.88 kacal daga kuɗin shigar mai.

N7tr aka samu alhali an yi hasashen samun Naira tiriliyan 18.65 a farkon rabin shekarar 2026.

Atiku ya ce hakan ya nuna an samu gibin Naira tiriliyan 10.77 tsakanin kuɗin da gwamnati ta yi hasashen samu da waɗanda ta tattara a bana.

An samu gibin duk da ƙarin kuɗin da ake samu daga sayar da ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Ya bayyana cewa bai kamata Tinubu ya ci gaba da ɗora wa 'yan Najeriya nauyin tsadar fetur ba, alhali gwamnatinsa ta kasa tattaro abin da aka yi niyya.

Ana zargin Bola Tinubu da jawo tsadar rayuwa

Ya ce tashin fetur ya ƙara kuɗin sufuri, yayin da tsadar dizal ke ƙara kuɗin samar da abinci da sauran kayayyaki, wanda hakan ya ƙara wahalar rayuwa.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani kan batun APC ta rubuta wasika ga INEC don tabbatar da nasarar Tinubu

‘Dan siyasar yana ganin wannan ya sa 'yan Najeriya ke fuskantar matsin lamba a cewar Daily Post.

Ganin gwamnati ba ta samun kuɗin shigar da ta yi tsammani ba, ya nemi Gwamnatin Tinubu ta yi wa al’umma bayanin inda ragowar kudin suka shiga.

Wannan buƙatar ta Atiku na zuwa ne bayan da NNPCL ta yi watsi da zarge-zargen da suka shafi ɓacewar $2.04b na jigilar jigilar ɗanyen mai da aka yi.

A cewar rahotannin, farashin fetur a Najeriya ya ci gaba da yin tsada tun kafin ɓarkewar yaƙin da ya shafi Iran da kasashen Amurka da kuma Isra'ila.

Atiku ya ce rahoton ofishin kasafin kuɗi ya nuna akwai matsalolin samar da ɗanyen mai da ƙarancin kuɗin da ake samu da gibi da ake yi wa lalitar.

Shi yana zargin akwai wasu kuɗin da ake cirewa kafin a tura ragowar dukiyar zuwa asusun tarayya.

Bayanan da Atiku ya nema daga gwamnatin Tinubu

Saboda haka, ya buƙaci gwamnatin Tinubu ta fitar da cikakken bayani kan:

  • Adadin ɗanyen man da Najeriya ta haƙo.
  • Yawan man da aka ɗauka domin sayarwa a kasuwannin duniya.
  • Jimillar kuɗin da aka samu daga sayar da man.
  • Kuɗin da aka cire kafin tura ragowar zuwa asusun tarayya.
  • Matakan da gwamnati ke ɗauka wajen magance satar ɗanyen mai da matsalar tsaron bututun mai.
  • Yadda za a magance ƙarancin jarin da ake zubawa a ɓangaren man fetur.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnoni 5 suka yi wa Atiku buƙulu, aka hana PDP samun nasara a zaben 2023

‘Dan takaran ya ce za a yi amfani da kudin da yake zargin an wawushe wajen gina makarantu, samar da kayan aiki a asibitoci da gyaran hanyoyi.

Da yake tallata jam’iyyarsu ta ADC, ya ce Tinubu yana da alhakin yi wa 'yan Najeriya cikakken bayani kan inda aka kai kuɗin da ake samu daga mai.

Ya ce idan suka ta karɓi mulki, za ta tabbatar da gaskiya da riƙon amana domin alfanun hakan ya isa ga gidaje, manoma, masu sufuri da 'yan kasuwa.

Tinubu da Remi
Shugaban kasa Bola Tinubu da mai dakinsa wajen yakin zabe Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnoni rututu suke tare da Tinubu

An ji cewa Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF), Hope Uzodimma, yana ganin Bola Tinubu zai zarce.

Ya tabbatar da cewa gwamnonin ƙungiyar su 31 na nan daram a bayan shugaban kasar duk da yaɗa farfaganda.

Uzodinma ya ƙara da cewa shugabancin Tinubu ya bai wa gwamnatocin jihohi damar farfaɗo da tattalin arzikinsu da kuma gina ababen more rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng