Wasu Ma'aikata Sun Shiga Uku, Gwarzo Ya Yi Masu 'Barazana' Idan Ya Yi Nasara a Kano
- Jam'iyyar APC ta Kano ta kalubalanci NDC kan zargin sanya farfesoshi da likitoci 26 cikin tawagar yakin neman zaben jam'iyyar
- APC ta bukaci dan takarar gwamnan NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya yi karin bayani kan barazanar da ake zargin ya yi wa ma'aikatan gwamnati
- Jam'iyyar ta yi gargadin cewa bai kamata a yi amfani da siyasa wajen tsoratarwa, gallazawa ko hana ma'aikatan gwamnati hakkokinsu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jam'iyyar APC a Kano ta kalubalanci jam'iyyar NDC da ta bayyana matsayin aikin farfesoshi da likitoci 26 da ake zargin suna cikin tawagar yakin neman zabenta.
Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa dan takarar gwamnan NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi gargadi ga ma'aikatan gwamnati da sunayensu suka fito cikin jerin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC.

Source: Twitter
A martaninta, APC ta tambayi NDC ko tana amfani da irin wannan mataki ga mutanen da ke cikin tawagar yakin neman zabenta, cewar Tribune.
APC ta dura kan Aminu Gwarzo
A cikin wata sanarwa da Sanusi Majidadi Kiru, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da gwamna na APC a Kano, ya sanya wa hannu, jam'iyyar ta yi nuni da wani takarda da ke yawo mai taken "NDC Kano State Professors and Doctors".
Kiru ya yi zargin cewa wasu daga cikin mutane 26 da ke cikin jerin ma'aikata ne a jami'o'in gwamnati da sauran hukumomin gwamnati.
Ya ce:
"Muna kira ga shugabannin NDC da su fito fili su yi karin bayani kan wadannan bayanan aikin mutanen."
APC ta bayyana cewa ba ta kalubalantar 'yancin wadannan mutane na shiga siyasa ba ne, sai dai tana bukatar a rika amfani da dokokin da suka shafi shigar ma'aikatan gwamnati cikin harkokin siyasa cikin adalci.
Kiru ya nuna damuwa cewa kalaman da ake dangantawa da Aminu Gwarzo na iya jefa ma'aikatan gwamnati cikin hadarin korar da ta shafi siyasa, sauya musu wurin aiki, hana su karin girma ko kuma shirya musu tuhumar ladabtarwa idan NDC ta karbi mulki.
Ya ce:
"Ma'aikatan gwamnati na jihar ne da al'ummarta, ba na kowace jam'iyyar siyasa ba.
"Ma'aikatan gwamnati kwararru ne da aka dora wa nauyin gudanar da ayyukan jama'a, don haka bai kamata a danganta hakkokinsu na aiki da ra'ayin siyasar duk wanda ya dare kan mulki ba."

Source: Original
Abin da doka ta ce kan lamarin
Sai dai Kiru ya amince cewa dokokin aikin gwamnati sun sanya takunkumi kan wasu nau'ikan shiga harkokin siyasa kai tsaye ga ma'aikata, yana mai cewa bai kamata a rika amfani da dokokin ne kawai wajen hukunta abokan hamayyar siyasa ba.
APC ta bukaci Gwarzo da ya fito fili ya yi karin bayani kan kalamansa tare da tabbatar wa ma'aikatan gwamnati cewa ba za a yi barazana ga ayyukansu ko ci gaban matsayinsu saboda ra'ayinsu na siyasa ba, cewar Punch.
Haka kuma, jam'iyyar ta jaddada cewa idan ana zargin wani ma'aikacin gwamnati da aikata ba daidai ba, ya kamata hukumomin da doka ta ba iko su gudanar da bincike bisa ka'ida da bin tsarin shari'a, ba bisa son zuciyar siyasa ba.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: An yi hasashen abin da mutanen jihohi 22 za su yi wa Tinubu a zaben 2027
ADC ta cire kwamitin kamfen a Kano
Kun ji cewa NDC ta ba shugaban NNPP na Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, babban muƙami a tawagar da za ta jagoranci yaƙin neman zaɓenta.
Sunan Dungurawa na cikin waɗanda aka zaɓa domin tafiyar da shirye-shiryen kamfen ɗin jam’iyyar na shugaban ƙasa da ta gwamnan Kano.
Jam’iyyar ta kuma ɗora wa Shehu Wada Sagagi alhakin jagorantar kwamitin, yayin da Sunusi Usman Dambatta zai taimaka masa.
Asali: Legit.ng

