Kotu Ta Shiga Maganar Gwarzo da Mambobin NDC ke Neman Hana Shi Takara a Kano
- Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta amince da bukatar shigar da Aminu Gwarzo cikin karar da ake yi kan tikitin takarar gwamnan jihar
- Wasu mambobin NDC uku ne suka shigar da karar domin hana jam’iyyar mika sunan Gwarzo ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa
- Gwarzo ya samu tikitin takarar gwamnan Kano na NDC, inda dan tsohon gwamnan jihar, Mustapha Kwankwaso, ya zama abokin takararsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta amince da shigar da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo, cikin karar da ake yi kan tikitin takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC.
Mai shari’a Simon Amobeda ne ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, 2026, bayan lauyan Gwarzo, Sagir Gezawa (SAN).

Source: Twitter
Ya gabatar da bukatar shigar da wanda yake karewa cikin karar a matsayin wanda ya kamata ya kasance cikin wadanda ake kara, cewar Punch.
Dalilin shigar da karar kan tikitin Gwarzo
Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa wasu mambobin NDC uku a Kano ne suka shigar da karar, inda suke neman kotu ta hana jam’iyyar gabatar da sunan dan takararta na gwamna ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Masu karar, Garba Umar Isa, Yau Abubakar da wani mamban jam’iyyar, sun kuma bukaci kotu ta hana INEC wallafa sunan Gwarzo a matsayin dan takarar gwamnan Kano na NDC.
Sun ce suna kalubalantar sahihancin tikitin ne bisa hukuncin da Kotun Koli ta yanke a shari’ar jam’iyyar Zenith Labour Party.
Yadda Gwarzo ya samu tikitin NDC
Aminu Gwarzo ya samu tikitin takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, inda aka tsayar da Mustapha Rabiu Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.
Sai dai INEC ta cire sunayen Gwarzo da abokin takararsa daga cikin jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da ta wallafa, bisa umarnin wata kotu.
A yayin zaman kotun na ranar Litinin, lauyan masu karar, Moses Falana, ya fara nuna adawa da bukatar shigar da Gwarzo cikin shari’ar.
Sai dai daga baya ya janye takardar adawarsa bayan ya sake duba bukatar da lauyan Gwarzo ya gabatar.
Abin da kotu ta yanke
A hukuncinsa, Mai shari’a Amobeda ya amince da bukatar, inda ya sanya Gwarzo a matsayin wanda ake kara na uku a shari’ar.
Alkalin ya ce:
“An amince da bukatar shigar da shi cikin shari’ar. An shigar da mai neman wannan bukata a matsayin wanda ake kara na uku.”
Daga nan sai ya umarci dukkan bangarorin da ke cikin shari’ar da su gabatar da takardunsu bisa sabon tsarin da ya kunshi shigar da Gwarzo cikin karar.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Satumba domin sauraron wasu bukatu na farko da har yanzu ba a kammala ba.
INEC ta magantu kan cire sunan Gwarzo
An ji cewa INEC ta ce ta tantance tare da amincewa da takarar Abdulsalam Gwarzo na NDC a zaben gwamnan Kano na 2027.
Hukumar ta bayyana cewa umarnin kotun tarayya da ke Kano na ranar 27 ga Oktoba ne ya hana ta wallafa sunan Gwarzo da mataimakinsa.
INEC ta amince da korafe-korafe 66, ta kuma yi watsi da wasu 64 da suka shafi ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi.
Asali: Legit.ng


