Rai Bakon Duniya: Ɗan'uwan Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamnan Jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang, ya rasa ɗan’uwansa, Arc. Morris Manasseh Mutfwang, wanda ya rasu a daren Lahadi
- Mataimakiyar gwamnan jihar, Ngo Josephine Piyo, da majalisar addinai ta jihar Filato sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan gwamnan a Jos
- Iyalin mamacin sun bayyana cewa za a yi jana’izarsa ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Gwamnan Jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang, ya rasa yayansa, Arc. Morris Manasseh Mutfwang, wanda ya rasu a daren Lahadi bayan fama da doguwar jinya.
Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da rasuwar yayan gwamnan a ranar Litinin, yayin da majalisar zartarwa da kuma Majalisar Addinai ta Jihar Filato suka kai ziyarar ta’aziyya a gidan gwamnati da ke Jos.

Source: Facebook
Gwamnatin Filato ta tura tawaga
Vanguard ta ruwaito cewa mataimakiyar gwamnan jihar, Ngo Josephine Piyo, ce ta jagoranci mambobin majalisar zartarwa ta jihar Filato wajen kai ziyarar ta’aziyya a gidan gwamnan da ke tsohon gidan gwamnati a Jos.
Yayin ziyarar, Piyo Ta bayyana mamacin a matsayin “mutum mai daraja, mai kishin iyalinsa, mai son zaman lafiya kuma ɗan Najeriya mai kishin ƙasa wanda ya bayar da gudummawa mai ma’ana ga ayyukan hidimar jama’a.”
Ta ce majalisar ta samu labarin rasuwarsa “cikin matuƙar alhini da jimami,” inda ta bayyana cewa mutuwarsa ba babban rashi ba ne ga iyalan Mutfwang kadai ba, har ma da Jihar Filato da ƙasa baki ɗaya.
Piyo ta yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamacin, sannan ta roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba gwamnan, iyalansa da duk waɗanda ke jimamin rasuwarsa ƙarfin hali da juriyar jure wannan babban rashi.
Majalisar addinai ta yi ta’aziyya
A wata ziyara ta daban, Majalisar Addinai ta Jihar Filato ita ma ta kai ziyarar ta’aziyya ga gwamnan da danginsa bisa rasuwar Arc. Morris Manasseh Mutfwang.
Tawagar, wadda Sarkin Wase, Alhaji (Dr.) Muhammadu Sambo Haruna, ya jagoranta, ta yi magana ne a madadin shugaban Rev. Prof. Pandam Yamsat. Haruna ya bayyana rasuwar mamacin a matsayin babban rashi mai radadi.
Haruna ya amince cewa mutuwa wani abu ne da babu makawa a rayuwar ɗan Adam, inda ya bukaci iyalan mamacin da su “samu kwanciyar hankali ta hanyar dogaro da ikon Allah Maɗaukakin Sarki da hikimarsa.”
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba iyalan ta’aziyya, ƙarfin hali da juriya da za su taimaka musu wajen shawo kan wannan mawuyacin lokaci.
Iyalai sun gode da ziyarar
Da yake mayar da martani a madadin danginnmamacin yayin ziyarorin ta’aziyyar, Mista Jonathan Mutfwang ya bayyana “matukar godiyarsu ga tawagogin biyu bisa kulawa, nuna goyon baya da addu’o’in da suka yi.”
Ya ce zuwansu ya kawo “babban ta’aziyya da ƙarfafa gwiwa ga dangin mamacin a wannan mawuyacin lokaci.”
Jonathan ya kuma yi addu’ar Allah Ya ci gaba da kare mambobin tawagogin, Ya albarkace su kuma Ya kiyaye su.
Iyalin sun bayyana cewa za a yi jana’izar marigayi Arc. Morris Manasseh Mutfwang ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng

