Zaben 2027: ADC Ta Bayyana Matsayarta kan Takarar Atiku duk da Hukuncin Kotu

Zaben 2027: ADC Ta Bayyana Matsayarta kan Takarar Atiku duk da Hukuncin Kotu

  • ADC ta dage cewa Atiku Abubakar zai kasance cikin ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da hukuncin kotu da ya soke takararsa
  • Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, Phrank Shaibu, ya yi iƙirarin cewa Atiku zai doke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen
  • Jam’iyyar ta shigar da ƙara mai dalilai 17 a Kotun Ɗaukaka Ƙara, tana ƙalubalantar hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya yanke ranar 5 ga Nuwamban 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta dage cewa Atiku Abubakar zai tsaya takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027, duk da hukuncin kotu da ya soke takararsa.

Jam’iyyar ta kuma yi iƙirarin cewa Atiku zai samu gagarumar nasara a zaɓen, duk da ƙalubalen shari’a da ya dabaibaye shugabancinta da shirye-shiryenta na zaɓen mai zuwa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kotu ta raba gardama kan tikitin takarar mawakin Kwankwasiyya a Kano

ADC ta yi magana kan takarar Atiku a 2027
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro a Bauchi Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Daraktan yaɗa manufofi da sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa a shirin The Morning Brief na Channels Tv ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026.

ADC ta ce Atiku zai doke Tinubu

Maganar ta biyo bayan hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya yanke ranar 5 ga Nuwamba, a ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar.

Hukuncin ya jefa tsarin shugabancin ADC da shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027 cikin sabon ƙalubalen shari’a.

Sai dai da yake mayar da martani kan soke takarar Atiku, Shaibu ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai kasance cikin ’yan takarar da za a saka a takardar zaɓe.

Ya kuma yi iƙirarin cewa Atiku zai doke Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar APC mai neman sake zaɓe.

A kalamansa:

“Ra’ayina a bayyane yake, babu ruɗani a ciki. Yaƙin neman zaɓenmu na samar da rayuwa mai sauƙi yana isa ga kowane lungu da saƙo na Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

“Atiku Abubakar zai kasance cikin ’yan takarar da za a saka a kuri'ar zabe, kuma ba kasancewa kawai zai yi ba; zai yi wa Bola Ahmed Tinubu mummunan rinjaye a ranar 16 ga Janairun 2027.”

Jam’iyyar ADC ta ɗaukaka ƙara

Kakakin ADC ya bayyana cewa jam’iyyar ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda ta nemi a hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sauya bayanan shugabancinta da kuma bayanan takarar Atiku.

Ya ce sun kuma nemi kotun ta hana INEC yin wani sauyi ga bayanan ’yan takarar gwamnan da jam’iyyar ta tsayar har sai an yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da suka shigar.

A cewarsa, ADC ta gabatar da dalilai 17 na ƙalubalantar hukuncin ranar 5 ga Nuwamban 2026, wanda ta bayyana a matsayin hukunci mai manyan kura-kurai.

Jam’iyyar mai adawa a Najeriya ta yi zargin cewa kotun farko ba ta da ikon sauraron rikicin shugabancinta.

ADC ta yi magana kan takarar Atiku
Alhaji Atiku Abubakar na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Fashola ya kalubalanci Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babatunde Fashola, ya kalubalanci Atiku Abubakar da ya yi bayani kan yadda zai samar da kuɗaɗen dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.

Tsohon ministan ya bayyana shirin tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin wanda ba shi da tushe mai ƙarfi, yana mai cewa Atiku bai yi cikakken bayani kan matsalolin da ka iya kawo cikas ga aiwatar da shirin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng