Shugaban APC, Daraktan Kamfe Sun Gamu da Hatsarin Mota yayin Gangamin Siyasa

Shugaban APC, Daraktan Kamfe Sun Gamu da Hatsarin Mota yayin Gangamin Siyasa

  • Shugaban APC a Gombe, Mohammed Ndus, da daraktan yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar na 2027, Sa’adu Hassan, sun jikkata a hatsarin mota
  • Hatsarin ya faru ne yayin da jami’an jam’iyyar ke kan hanyarsu ta zuwa gangamin yaƙin neman zaɓen Gwamna Inuwa Yahaya a Balanga ta Arewa
  • An garzaya da jami’an biyu zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe, inda ake ba su kulawar likitoci bayan hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Balanga, Gombe - Shugaban APC a Gombe, Mohammed Ndus, da daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar na 2027, Sa’adu Hassan, sun ji rauni a hatsarin mota.

Hatsarin ya rutsa da su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen taron yaƙin neman zaɓen gwamnan Gombe a ƙaramar hukumar Balanga.

An garzaya da jami’an jam’iyyar biyu zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe domin ba su kulawar likitoci, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da ya fi burge Atiku idan aka taɓa Tinubu yayin amfen

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne jim kaɗan bayan jami’an APC ɗin sun bar cikin birnin Gombe domin haɗuwa da tawagar motocin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da ke kan hanyarsu ta zuwa taron yaƙin neman zaɓe a Balanga ta Arewa.

Shugaban APC ɗin, Mohammed Ndus, ya samu munanan raunuka, yayin da Sa’adu Hassan ya samu ƙananan raunuka.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) a Gombe, Samson Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya samu labarin hatsarin.

Sai dai ya bayyana cewa har yanzu yana tattara cikakkun bayanai kan yadda hatsarin ya faru da kuma halin da waɗanda abin ya shafa suke ciki.

Bayanan farko sun nuna cewa hatsarin ya faru ne bayan wani mai babur ya fito kwatsam a kan hanya, lamarin da ya tilasta wa direban motar da shugaban APC ɗin yake ciki kaucewa domin guje wa karo.

Motar ta kauce daga kan hanya a lokacin da direban ke ƙoƙarin kauce wa babur ɗin.

Taron yaƙin neman zaɓen na Balanga ta Arewa na daga cikin shirye-shiryen APC na neman goyon bayan jama'a gabanin zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan halin da jami'an biyu suke ciki ba.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya ware gwamnonin Arewa 7, ya ba su shawara kan goyon bayan Tinubu a 2027

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.