Ana Shirin 2027, Tinubu zai Raba Tallafin Naira Biliyan 45
- Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta APC ta ce Shugaba Bola Tinubu ya ware Naira biliyan 450 domin shirye-shiryen tallafa wa manoma
- Ta kuma bayyana cewa Tinubu ya amince da sake zuba jarin Naira tiriliyan 1.5 a Bankin Aikin Gona domin faɗaɗa damar samun rance da tallafin noma
- Kwamitin ya ce shirye-shiryen sun riga sun amfani manoma ƙanana sama da 500,000 a jihohi 16, ciki har da mata fiye da 70,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 450 domin shirye-shiryen samar da kuɗin tallafa wa harkokin noma a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Dele Alake, ya fitar, ta ce shugaban ƙasar ya kuma amince da sake zuba jarin Naira tiriliyan 1.5 a Bankin Aikin Gona (BoA).

Source: Facebook
Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook cewa matakan na da nufin ƙarfafa samar da abinci a ƙasar, bunƙasa noman cikin gida da kuma inganta ayyukan manoma ƙanana, musamman a Arewacin Najeriya.
An ware N200bn ga manoma
Kwamitin ya ce Bankin Aikin Gona na aiwatar da shirin Guaranteed Minimum Price Programme na Naira biliyan 200 domin kare manoma daga faɗuwar farashin amfanin gona.
A ƙarƙashin shirin, bankin noma ya sayi tan 170,000 na masara, shinkafa, dawa da rogo domin ƙarfafa kasuwannin amfanin gona da hana manoma sayar da kayayyakinsu cikin asara.
Haka kuma, bankin ya ƙaddamar da shirin tallafa wa masu noman albasa tare da haɗin gwiwar ƙungiyar NOPPMAN, wadda ke wakiltar manoman albasa sama da 11,800.
Shirin na samar da ingantattun iri da takin zamani ga manoma, kuɗin sayen albasa ga masu sarrafawa da kuma wuraren ajiya masu amfani da hasken rana domin rage ɓarnar amfanin gona.
Za a ba manoma tallafi
Punch ta rahoto cewa APC-PCC ya ce Bankin Aikin Gona na aiki da ƙungiyar manoma ta ƙasa domin tallafa wa manoma 400,000 a noman rani na shekarar 2026.
Shirin ya ƙunshi samar da kuɗin noma a hekta 120,000 na alkama da wasu hekta 300,000 domin noman shinkafa, masara, dawa, gero, rogo da waken soya.

Source: Getty Images
Sanarwar ta kuma ce an rarraba taraktoci 1,571 zuwa jihohi 23 a ƙarƙashin shirin Renewed Hope National Agricultural Mechanisation Programme, da nufin taimakawa wajen noma a hekta miliyan 1.2.
Bugu da ƙari, majalisar ta ambaci shirin samar da kayayyakin amfani da lantarki na Naira biliyan 385, wanda ya haɗa da adaidaita sahu masu ɗaukar kaya 44,000 da famfunan ban-ruwa masu amfani da hasken rana 100,000.
Tinubu zai raba taki
A wani rahoton, kun ji cewa Kashim Shettima ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a masana’antar takin zamani da su gaggauta shirye-shiryen samar da buhunan takin sama da miliyan 3.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Jam'iyyar adawa ta yanke shawara, ta umarci mabiyanta su zaɓi Tinubu a 2027
Umarnin ya biyo bayan amincewar Shugaba Bola Tinubu da samar da kudin a ƙarƙashin shirin Renewed Hope na noma domin rage tsadar takin zamani da bunƙasa noman abinci.
Shettima ya bayar da umarnin ne yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin takin zamani a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a makon d ya wuce.
Asali: Legit.ng

