NDC Ta Nada ‘Dan Shekara 50 Ya Zama Darakta Janar a Kamfen Obi da Kwankwaso
- Jam’iyyar NDC mai hamayya ta fitar da sunayen ‘yan kwamitin yakin zaben shugaban kasa
- Ibrahim Hussain Abdulkarim shi ne Darekta Janar na tallar tikitin Peter Obi/Rabiu Kwankwaso
- Ana sa ran rantsar da kwamitin yakin neman zaben a Abuja ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar NDC ta kafa kwamitin yakin neman zabenta na kasa domin babbar takarar da za a yi a shekarar 2027.
Kwararren masani kan fasahar sadarwa ta zamani (ICT), Mallam Ibrahim Hussain Abdulkarim aka nada Darekta Janar.

Source: Twitter
Jam'iyyar NDC ta hada Ibrahim Abdulkarim da kamfe
Jam’iyyar hamayyar ta saki sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ne a dandalin X ranar 25 ga Oktoba.
Ikenna Enekweizu, sakataren jam’iyyar na kasa shi zai zama sakataren kwamitin, yayin da matashin zai jagoranci kamfen din.
Ibrahim Abdulkarim haifaffen Sokoto ne da yake rayuwa a Kaduna. Shi ne shugaban kamfanin EasyGIS Nigeria Limited.
Darekta Janar din mai shekara 50 yana cikin manyan masoyan Peter Obi. Ya so ya nemi takarar gwamna amma ya hakura.
Shugabannin kwamitin yakin zaben NDC
Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, zai jagoranci kwamitin tare da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Shugaban NDC na kasa, Sanata Cleopas Zuwoghe, shi ne mataimakin shugaban kwamitin tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
NDC ta ce kwamitin zai jagoranci yakin neman zabe mai mayar da hankali kan bukatun jama’a da manyan batutuwan da suka shafi kasa.
Jam’iyyar ta ce kwamitin zai tsara dabarun yakin neman zabe, daidaita ayyukan kamfe tare da wayar da kan ’yan Najeriya game da manufarsu.
A cikin sanarwar da jam’iyyar ta fitar ranar Lahadi, an ji cewa za a rantsar da kwamitin a Abuja a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, 2026.
An kuma kafa kwamitin ba da shawarwari mai mutum 40 da masu gudanar da yakin neman zabe a babban birnin Abuja da sauran jihohi 37.
Shugabannin kamfe na kasa:
- Henry Seriake Dickson
- Peter Obi
- Cleopas Moses Zuwoghe
- Rabiu Musa Kwankwaso
- Babachir Lawal
- Ikenna Morgan Enekweizu
- Sidi Bomi Abdul
- Babatunde F. Alli
- Ovie Omo-Agege
- Victor Umeh
- Ibrahim Hussain Abdulkarim
- Buba Galadima
- Yakubu Ochefu
- Mahmud Gambo Jahun
- Moshood Salvador
- Dudu Manuga
- Victor Ogene
- Muktar Usman
Majalisar mashawarta
- Moses Cleopas Zuwoghe
- Sam Egwu
- Ikenna Morgan Enekweizu
- Danladi Abdulhameed Tambari
- Onyema Ugochukwu
- Ini Okon
- Oseloka Obaze
- A. Mohammed
- O. O. Osusu
- Tor Ujah
- Ibrahim Alhaji S. Matawalle
- Ugba Murphy
- Pat Utomi
- Roland Owie
- Akinyede Sola
- Okwesilieze Nwodo
- Uche Okonkwo
- Iliya Ishaya Jalo
- Achike Udenwa
- Hassan Kabiru
- Joshua Makama
- Nasir Lawan Ahmad
- Ismail Iro
- Ahmed Zayyanu Iliyasu
- Adamu Atta
- Toma Audu Gana
- Tunji Soyinka
- David Zakaria
- Isa A. Kutugi
- Tope Niyi Taiwo
- Tope Adebambo
- Razaq Mustapha Adeniyi
- Kayode Joseph
- Manasseh Zakka Watyil
- Ben Birabi
- Jabbi Hassan Sifawa
- Philip Kafiya
- Buba Galadima
- Mohammed Sani Takori
Bangaren kamfe na kasa
- Ibrahim Hussain Abdulkarim
- Ebubedike VinMartin Obiora Ilo
- Tijjani Iya
- Fred E. Owotorufa
- Ndidi Mbagwu
- Peter Onigah
- Folashade Aliu
- Oseloka Obaze
- Wole Adedapo
- Ibrahim Tukur Gusau
- Osa Director
- Ikeddi Isiguzo
- Constance Ikokwu
- Sonny Neme
- Sam Omale
- Anulka Rita Modebe
- Wesley Gainaka
- Ibrahim Rabi’u Amana
- Nwosu Christopher Maduabuchukwu
- Isaiah Osifo
- Makinde Akinlade
- Zekeri Idris
- Theophilus Abu
- Obinna Simon
- S. K. C. Ogbonnia
- Shehu Muhammad Danmusa
- Reuben Egwuaba
- Vincent Otaokpukpu
- John Enenche
- Ali Garba Sarbi
- Danlami Arabs Rukujei
- Bilkisu Shu’aibu
- Daniel Elombah
- Maryam Tolofari Nyong
- Daniel Onifade
- Adamu Abbas Ahman
- Idris Usman Audu
- Dudu Manuga
- Binta Abba Gana
- Maji Peterx
- Abduljalal Idris
- Shu’aibu Abdulrashid
- Abayomi Kuye Taiwo
- Jackie Wayas
- Sharon Chukwuobasi
- Abdulrazak Maaji
- Umar Mahmood
- Malate Peter
- Chinasa Issac-Oduka
- Nafiu Umar Dankura
- Madaki Muhammad wMisau
- Umar Usman Besse
- Hart Sylvanus Idabelema Handley
- Abdulmutallib Alhassan
- Boma N. Williams
- Brian Jonah Dennis
- Pillar Josemaria
- Ezra Dablet
- Abdullahi Akilo Jugunnu
Jagororin kamfe a jihohi
- Nkechi Nwogu
- Bamanga Tukur Jr.
- David Okpon
- Ifeanyi Ibezim
- Sulaiman Muhammad
- Silva Opuala-Charles
- Andrew Abba
- Abdulkadir Fema
- Eta Mbora
- Ken Pela
- Ben Odoh
- John Yakubu
- Babafemi Adegbite
- Oscar Okwudili Ossai
- Garba Zagada Zagada
- Martins Agbaso
- Ado Waziri Kwalam
- Ibrahim Mado
- Abdullahi Musa
- Zayyana Shehu
- Ladan Soja Bunza
- Peter Ameh
- Anthony Dele Abiodun
- Ife Salako
- Abimbola Lanre-Balogun
- Idowu Famusipe
- Kunle Tiamiyu
- Adeola Ebisemiju
- Rwang Pam
- Zubi Nwuke
- Ibrahim Abubakar
- Abdullahi Ade
- Ilu Bello Dambazau
- Stephen Knabayi
INEC za ta yi zama kan batun takarar gwamna
A yanzu labari ya zo cewa Hukumar INEC za ta yanke hukunci kan makomar wasu ’yan takara da aka cire sunayensu a jerin karshe.

Kara karanta wannan
Sanata Yari ya fadi dalilin da ya sa tawagar kamfen din Tinubu ke ziyartar sarakuna
Masu neman shiga zaben gwamnonin 2027 da abin ya shafa sun hada Farfesa Isa Ali Pantami, Oladipupo Adebutu a jihar Ogun.
Akwai Aminu Abdussalam Gwarzo da ‘yan Kwankwasiyya suka yi tunanin zai yaki Abba Kabir Yusuf da aka ga babu labarin sunan shi.
Asali: Legit.ng



