Jita Jita Ta Kare, An Bayyana Abin da Aka Tattauna tsakanin Peter Obi da 'Yan Majalisar Amurka
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya yi karin haske kan ziyararsa ta baya-bayan nan a Washington DC
- Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce manufar ziyarar ita ce tattaunawa kan ci gaban Najeriya, jin daɗin 'yan ƙasa da makomar dimokuraɗiyyar ƙasar
- Obi ya yi kira ga shugabannin siyasar Najeriya da ke neman muƙaman gwamnati da su riƙa tattaunawa da ƙasashen duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC), Peter Obi, ya nesanta ziyarar da ya kai Amurka kwanan nan da neman goyon bayan takararsa a zaben 2027.
Peter Obi ya ce tattaunawar da ya yi da wasu 'yan majalisar wakilan Amurka a birnin Washington DC ba da nufin neman goyon bayansu ga takararsa ta shugaban ƙasa a 2027 ba.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.
Ya wannan bayani ne don mayar da martani kan rahotannin kafafen yaɗa labarai da suka nuna cewa ganawarsa da wasu 'yan Majalisar Dokokin Amurka na nufin sun amince da takararsa ta shugaban ƙasa.
Obi ya ce babban dalilin ziyararsa Amurka shi ne tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ci gaban Najeriya, jin daɗin 'yan ƙasa da kuma makomar dimokuraɗiyyar ƙasar.
Ya ce babu inda ya fito ya bayyana ganawar a matsayin amincewar Majalisar Dokokin Amurka ko wani daga cikin mambobinta ga burinsa na siyasa ba.
Ya ce:
“Kamar yadda na bayyana a fili a jawabina, ban je Amurka da niyyar neman amincewa ba, kuma ban bayyana ganawata a matsayin amincewar Majalisar Dokokin Amurka ko wani daga cikin mambobinta ga burina na siyasa ba.
“Abin da ya fi damuna shi ne ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya, inganta riƙon amana da tabbatar da cewa tsarin zaɓen Najeriya yana samar da zaɓuka masu 'yanci, adalci, gaskiya da sahihanci.

Kara karanta wannan
Da gaske Majalisar Amurka ta zaɓi wanda take goyon baya a zaben Najeriya? Bayanai sun fito
"Waɗannan batutuwa ya kamata su damu duk wani ɗan Najeriya da ya damu da makomar ƙasarmu.”
Peter Obi ya ja hanaklin yan siyasa
Ɗan takarar na NDC ya kuma ƙarfafa sauran shugabannin siyasar Najeriya, musamman waɗanda ke neman muƙaman gwamnati, da su riƙa tattaunawa da masu ruwa da tsaki na ƙasashen duniya kan batutuwan da suka shafi ƙasar.
Ya ce:
“Za a iya ƙarfafa dimokuraɗiyyarmu ta hanyar tattaunawa mai ma'ana, musayar ƙwarewa da kuma haɗin kai wajen tabbatar da sahihancin zaɓe.”

Source: Facebook
Majalisar Amurka ta goyi bayan Obi?
Kun ji cewa kamfanin masu yi wa 'yan siyasa ƙoƙarin samun goyon baya a Amurka, Von Batten-Montague-York, L.C., ya yi karin haske kan haduwar Peter Obi da wasu yan Majalisa.
Kamfanin, wanda ke yi wa Atiku aiki ya musanta ikirarin cewa Majalisar Dokokin ƙasar Amurka ta gana da Peter Obi ko kuma ta amince ta goyi bayan takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
