An Ba Yar Amurka Dala Miliyan 4.5 bayan Ta Yi Hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

An Ba Yar Amurka Dala Miliyan 4.5 bayan Ta Yi Hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

  • Masaniyar siyasa a Amurka, Diana London, ta musanta karɓar dala miliyan 4.5 daga gwamnatin Najeriya kan hirar da ta yi da Shugaba Bola Tinubu
  • Ta bayyana zargin a matsayin yaƙin ɓata mata suna, tana mai cewa babu wanda ya biya ta kuɗin a Najeriya
  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta bayyana alaƙar hirar da wata kwangila da aka ruwaito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Masaniyar harkokin siyasar Amurka kuma mai sharhi a kafafen yaɗa labarai, Diana London, ta musanta karɓar Dala miliyan 4.5 daga gwamnatin Najeriya kan hirar da ta yi kwanan nan da Shugaba Bola Tinubu.

Diana London ta bayyana zargin a matsayin yaƙin ɓata mata suna, tana mai jaddada cewa gwamnatin Najeriya ko wani mutum a ƙasar bai biya ta kuɗin da ake zargin ta karɓa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano dabarun 'yan kasuwa, za a kawo karshen kauce wa biyan haraji

Diana.
Diana London tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu jami'an Gwamnatin Najeriya Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

A wani sako da ta wallafa a shafin X, ta ce ta ziyarci Najeriya ne domin yin hira da Tinubu a wani shirin fim mai taken documentary, da kuma ganin ƙasaqr da idonta.

Da gaske an ba Diana London $4.5m?

Ta rubuta cewa:

“Ina musanta gaba ɗaya zargin cewa gwamnatin Najeriya ko wani mutum a Najeriya ya biya ni Dala miliyan 4.5. Na je Najeriya ne domin yin hira da Shugaba Tinubu a wani ɓangare na shirin documentary, da kuma ganin Najeriya da idona.
“Wannan yaƙin ɓata suna na iya yin tasiri, amma ba zai iya sauya gaskiya ko hana ni faɗin gaskiya ba.”

Musantawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan hirar da ta yi da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Talata.

Lamarin ya ja hankali ne bayan bullar wasu rahotannin da ke zargin tana da alaƙa da wani tsarin biyan kuɗi na dala miliyan 4.5 da ya shafi gwamnatin Najeriya a Amurka.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: 'Yar Amurka ta goge saƙonnin da ta fitar kan Tinubu da Najeriya

Atiku ya fara zargin fitar da kudin

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta fayyace ko hirar tana da alaƙa da kwangilar aikin talla da aka ruwaito, tare da bayyana cikakkun bayanan yarjejeniyar.

Atiku ya ce takardun da aka shigar a Amurka sun nuna cewa Diana London mai ba da shawara ce ga kamfanin DCI Group AZ, wanda rahotanni suka ce gwamnatin Najeriya ta ɗauka aiki ta hannun kamfanin Aster Legal.

Ya ce takardun sun nuna cewa DCI Group ta karɓi kuɗin farko na dala miliyan 4.5, amma ya jaddada cewa ya kamata fadar shugaban ƙasa ta bayyana ko hirar tana cikin ayyukan da kwangilar ta ƙunsa.

Sai dai Diana London ta fito ta musanta wannan zargi, tana mai cewa babu aanda ya ba ta wasu kudi saboda hirar da ta yi da Bola Tinubu.

Diana London ta goge sakonni

Kun ji cewa yar kasar Amurka ta goge sakonnin da ta wallafa game da hulɗarta da gwamnatin Najeriya da kuma haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, inda aka ce ta yi hira da Tinubu.

Da farko, Diana London ta wallafa hotunanta a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja tare da Shugaba Bola Tinubu da shugaban ma'aikatan fadar, Femi Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262