Wike vs Turaki: Babbar Kotu Ta Yi Hukunci kan Rikicin Shugabancin Jam'iyyar PDP

Wike vs Turaki: Babbar Kotu Ta Yi Hukunci kan Rikicin Shugabancin Jam'iyyar PDP

  • Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da karar neman INEC ta amince da kwamitin rikon kwarya na PDP karkashin Kabiru Turaki
  • Kotu ta bayyana cewa masu shigar karar ba su da hurumin shigar da ita a madadin jam'iyyar adawa ta PDP
  • Alkalin babbar kotun ya bayyana karar a matsayin maimaita batutuwan da kotuna suka riga suka yanke hukunci a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ke neman tilasta wa Hukumar Zabe (INEC) ta amince da kuma wallafa sunayen kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar PDP karkashin Tanimu Turaki.

Mai shari'a Salim Ibrahim, ya ce wadanda suka shigar da karar karkashin jagorancin shugaban Kwamitin Amintattu (BoT) na PDP, Adolphus Wabara, ba su da hurumin shigar da ita.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Kotu ta yi hukunci kan takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban ƙasa na 2027

Tanimu Turaki.
Shugaban tsagin jam'iyyar adawa ta PDP, Tanimu Turaki (SAN) Hoto: Tanimu Turaki
Source: Facebook

Kotu ta goyi bayan bukatar INEC

Tashar Channles tv ta ruwaito cewa kotun ta amince da bukatar farko da INEC ta gabatar, tare da amincewa da bukatun wasu bangarori da suka nemi shiga cikin karar.

Mai shari'ar ya ce masu karar sun kasa tabbatar da cewa INEC ta taba amincewa da kwamitin rikon kwaryar da Kabiru Turaki ke jagoranta ko kuma cewa suna da izinin wakiltar PDP a kotu.

Abin da masu kara suka nema

Mambobin Kwamitin Amintattu karkashin Wabara sun bukaci kotu ta umarci INEC ta sabunta bayananta tare da wallafa sunayen shugabannin rikon kwarya a shafinta na intanet.

Sun yi ikirarin cewa an aika wa INEC da sunayen shugabannin ta wasikun da aka rubuta ranar 4 ga Mayu, tare da cewa dokokin kundin tsarin mulkin PDP sun wajabta wa hukumar amincewa da su.

Kotu ta ce an riga an yanke hukunci

Kafin yanke hukunci na karshe, kotun ta amince da bukatar shiga karar da tsagin PDP da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike ya gabatar.

Kara karanta wannan

Bayan Malami, kotu ta bayar da umarnin kwace kadarorin N8.94bn a hannun 'yar kasuwa

Daga bisani, ta tabbatar da dukkan korafe-korafen farko tare da bayyana cewa karar ta kasance cin zarafin tsarin shari'a saboda tana kokarin sake bude batutuwan da kotuna suka riga suka yanke hukunci a kansu.

Kotu ta kuma cire sunan PDP daga cikin masu karar, tana mai cewa ba a ba wadanda suka shigar da karar izinin yin hakan a madadin jam'iyyar ba.

Tutar PDP.
Tutar jam'iyyar adawar Najeriya ta PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Kotu ta ayyana shari'ar da marar amfani

Mai shari'a Ibrahim ya ce karar ta zama marar amfani saboda hujjojin da aka gabatar sun nuna cewa INEC ta sa ido kan babban taron PDP da ya samar da shugabancin Abdulrahman Mohammed.

Ya ce:

"Kotuna ba sa yanke hukunci kan batutuwa na zato ko wadanda suka zama marasa amfani."

Tsagin Wike ya tura sunayen yan takara

Kun ji cewa tsagin jam’iyyar PDP da ke da goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya daura sunayen ‘yan takara na zaben da za a yi a shekarar 2027.

Bangaren Ministan Abuja sun bayyana cewa ‘yan tsaginsu ne suka samu shiga shafin INEC, kenan suke da halatattun masu yin takara.

Hakan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan Nyesom Wike ya yi magana, inda ya nuna cewa jam’iyyarsu ba za ta iya lashe zaben 2027 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262