Sule Lamido Ya Yi Magana kan Hadakar Atiku da Obi a 2027

Sule Lamido Ya Yi Magana kan Hadakar Atiku da Obi a 2027

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce rashin hadin kan Atiku Abubakar da Peter Obi yana kara wa Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaben 202
  • Lamido ya bayyana cewa da Atiku da Obi sun hada kai, da za su fi samun karfin kalubalantar Tinubu, inda ya ba da shawarar cewa Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa
  • Ya kuma yi gargadin cewa ko wane daga cikin manyan 'yan takarar ya lashe zaben, Najeriya ba ta da riba idan aka ci gaba da fifita burin siyasa kan hadin kan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya soki 'yan jam'iyyun adawa, Atiku Abubakar da Peter Obi, kan kasa hada kai gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Kara karanta wannan

Na gaban goshin Tinubu ya fadi wanda suke shakka a 2027, ban da Atiku da Obi

Lamido, jigo a jam'iyyar PDP, ya ce rabuwar kan 'yan adawar na kara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar lashe zaben mai zuwa.

Sule Lamido a wajen taro
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido. Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin wata hira da shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television.

Magana kan hadakar 'yan adawa

Da aka tambaye shi ko zaben 2027 zai iya zama kamar na 2023, inda Tinubu ya doke Atiku da Obi, tsohon gwamnan ya ce rashin hadin kan 'yan adawar na taimaka wa shugaban kasar.

Ya danganta hakan da yawan gwamnoni da tsofaffin gwamnoni da APC ke da su, tare da gazawar Atiku da Obi wajen hada karfinsu.

A cewarsa, da shugabannin biyu sun hada kai, da sun samar da gagarumin kalubale ga Tinubu.

Sule Lamido ya ce Atiku zai iya zama dan takarar shugaban kasa, yayin da Obi zai zama mataimakinsa, sannan bayan shekaru hudu su sake duba yadda za a mika mulki tsakaninsu.

Atiku Abubakar da Peter Obi
Peter Obi a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Mr Peter Obi|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Magana kan cigaban kasa

Sule Lamido ya bayyana damuwarsa kan yadda takarar shugabancin kasar ke kara zama na kashin kai, inda manyan 'yan siyasa ke sukar juna maimakon tattauna hanyoyin magance matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jero dalilai 4 da suka sa zai yaƙi Tinubu a 2027 duk da ya goyi bayansa a 2023

Ya ce:

“Na dade ina cewa, duk wanda ya ci zabe, Najeriya za ta yi asara. Wannan shi ne abin da ke damuna.
“Ko Peter Obi ne ya ci, ko Atiku, ko wani daban, hadin kanmu, tattalin arzikinmu da kaunar da muke yi wa juna a matsayin 'yan uwa, duk sun rushe. Yanzu abin ya fi karkata ga ra'ayoyin kashin kai. Suna cin zarafin juna, har al'amarin ya zama na kashin kai.”

Ya kara da cewa siyasar kasar ta kauce daga tattaunawa kan ci gaban kasa, hadin kai da irin abubuwan da 'yan takara za su iya yi wa al'umma.

INEC za ta yi zaben gwaji

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da shirinta na gudanar da gwajin kada kuri'a a fadin Najeriya ranar 28 ga Nuwamba domin shirin zaben 2027.

Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ne ya sanar da hakan yayin wani taron tattaunawa kan makomar dimokuradiyyar Najeriya a cibiyar Chatham House da ke birnin Landan.

Ya ce za a yi amfani da gwajin wajen tantance ingancin na'urar BVAS da aka inganta, tsarin tantance masu kada kuri'a da kuma aika sakamakon zabe ta intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng