Makinde Ya Faɗi dalilin Ƙalubakantar Tinubu duk da Sun Fito daga Yanki Ɗaya
- Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya kare matakin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, duk da kasancewar Bola Tinubu daga Kudu maso Yamma
- Makinde ya tuna cewa yankin ya taɓa samar da ’yan takara biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 1999, ba tare da matsala ba
- Ya ce zai mayar da hankali kan ƙwazo da kuzari a yaƙin neman zaɓe, tare da sukar gwamnatin tarayya kan yadda take gudanar da kasafin kuɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnan Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya kare matakin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Ya ce Kudu maso Yamma na iya samar da ’yan takarar shugaban ƙasa fiye da ɗaya ba tare da hakan ya cutar da muradun yankin ba.

Source: UGC
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin taron jama’a na jam’iyyarsa a Kudu maso Yamma, wanda aka gudanar a Akure, babban birnin Ondo, cewar Punch.
Yawan tambayoyi da ake yi wa Makinde
Ya bayyana cewa wasu mutane sun tambaye shi dalilin tsayawa takara, ganin cewa yankin Kudu maso Yamma ya riga ya samu shugaban ƙasa.
Makinde ya ce ya bayyana musu cewa akwai misalin da ya faru a yankin a baya, wanda ke nuna cewa babu laifi a samar da ’yan takara biyu.
Ya tuna cewa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999, yankin ya samar da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma Olu Falae, waɗanda suka fafata.
Ya ce:
“Kuma sama ba ta faɗo ba. A maimakon haka, abin da Kudu maso Yamma ya yi shi ne gabatar da fitattun ’yan takararsa biyu ga Najeriya domin jama’a su zaɓa. Shin akwai laifi a yin haka a wannan karon?”

Kara karanta wannan
Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?

Source: UGC
Shawarar Gwamna Makinde ga masu zabe
Gwamnan ya kuma buƙaci masu zaɓe a yankin da su ƙi amincewa da siyasar yaudara, yana mai cewa zai fi mayar da hankali kan nasarorin da ya samu a Oyo maimakon sukar abokan hamayyarsa kawai.
Makinde ya soki gwamnatin tarayya kan rahoton cewa wakilan Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya sun kawo kasafin kuɗin majalisar ga shugaban ƙasa a Najeriya.
Ya tambayi dalilin kashe kuɗin masu biyan haraji wajen biyan kuɗin tafiya daga birnin New York zuwa Abuja, cewar Vanguard.
Gwamnan ya kuma yi tambaya game da yadda gwamnati ke aiwatar da kasafin kuɗi, inda ya ce: “Shin kasafin kuɗin shekarar 2023 ne, 2024, 2025 ko kuma 2026?”
Da yake ci gaba da jawabi, Makinde ya ce zai mayar da hankali kan kuzari da ƙwazo maimakon shekaru a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Ya ce:
“Duk da cewa ba zan mayar da shekaru batun yaƙin neman zaɓena ba, zan mayar da hankali kan kuzari. Samun kuzari da iya yin aiki har cikin dare, jure wahalhalun aiki da kuma samun ƙarfin tunkarar ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta.”
Makinde ya ƙalubalanci sauran ’yan takarar shugaban ƙasa da su nuna ƙarfinsu na jiki yayin yaƙin neman zaɓe.
Makinde ya zargi gwamnatin Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Seyi Makinde ya zargi APC da ƙoƙarin hana jam’iyyun adawa haɗa kai, yana mai cewa ya kamata al’ummar Kudu maso Kudu su kwato abin da ya kira ikon zaɓensu.
Gwamnan ya bayyana cewa yana da yakinin jam’iyyar APM za ta samu goyon bayan al’ummar yankin a zaɓe mai zuwa.
Makinde ya soki wasu manufofin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa shirye-shiryen CNG da da ɗanyen mai a Naira ba su kawo sauƙin sufuri ga ’yan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng

