Wata Sabuwa Ta Bullo, Ana Zargin Wasu Mutane na Yaudarar Tinubu gabanin Zaben 2027
- Shugaban jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi wasu na kusa da Shugaba Bola Tinubu da ba shi bayanan ƙarya
- Ya ce wasu gwamnoni da masu biyayya ga jam’iyya mai mulki na iya yaudarar shugaban ƙasar maimakon su saurari ra’ayin talakawa
- Baba-Ahmed ya danganta rashin gamsuwar jama’a da talauci, rashin kyakkyawan tafiyar da tattalin arziki, cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi ’yan siyasa da yaudarar Shugaba Bola Tinubu kan irin goyon bayan da gwamnatinsa ke samu daga jama’a.
Baba-Ahmed, wanda ya taɓa aiki a gwamnatin Tinubu a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, ya ce mutanen da ke kusa da shugaban ƙasar na iya yaudararsa.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya je Maiduguri, ya fito da abubuwa 3 da za su sa 'yan Arewa su nemi canji a 2027

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata tattaunawa a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels Television.
Ana zargin ana fadawa Tinubu karya
Ya ce wasu na jikin Tinubu na iya sa shi ya ɗauka cewa yana da farin jini sosai, ta hanyar dogaro da tabbacin gwamnoni da masu biyayya ga jam’iyya maimakon sauraron ra’ayoyin talakawa.
Shugaban PRP ya ce matsayar da ya ɗauka kan ra’ayin jama’a ta samo asali ne daga alaƙar siyasar da yake da ita da talakawa, da kuma sanin da yake da shi kan gwamnatin, wadda tun farko ya goyi bayanta.
“Ni ɗan siyasa ne, ina jagorantar jam’iyyar siyasa wadda tushenta yake a tsakanin talakawa, ina da alaƙa ta kai tsaye da jama’a. Na bibiyi gwamnatin Tinubu tun daga farkonta, a farko ma, ina cikinta,” in ji shi.
Baba-Ahmed ya ce ya san yadda ’yan Najeriya ke ji, kuma ba ya ƙara gishiri kan yadda rashin gamsuwa da gwamnati ya bazu a tsakanin jama’a.

Kara karanta wannan
Ayarin Shugaba Tinubu ya jefa mutane cikin babbar matsala ta taawon lokaci a Abuja
Abubuwan da ke damun 'yan Najeriya
Ya bayyana talauci, rashin kyakkyawan tafiyar da tattalin arziki, cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro a matsayin wasu daga cikin matsalolin da ke ƙara raba gwamnati da al’umma.

Source: Facebook
Ya kuma nuna cewa wasu na kusa da shugaban ƙasar na ba Tinubu tabbacin cewa zai iya samun nasara a 2027, ba tare da la’akari sosai da yadda ’yan Najeriya ke kallon gwamnatinsa ba.
“Akwai mutane da dama da ke yi wa Shugaba Tinubu ƙarya idan har shi da kansa, da su ma, suna ganin cewa jama’a na tare da su. A duba duk inda APC ta je. Ko dai mutane su kore su ko kuma su jawo tashin hankali,” in ji shi.
PRP ta soki Shugaba Tinubu
Kun ji cewa jam’iyyar PRP ta soki shirin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu, tana zargin gwamnatinsa da gaza magance matsalar rashin tsaro da talauci.
Shugaban PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce ’yan Najeriya za su ci gaba da neman kariya daga masu garkuwa da mutane da masu kisan kai.
Asali: Legit.ng