Lauya Ya ga Ta Kansa a Kano da Wata Mata Ta Ciji Ɗan Sanda a kotu
- Wata kotun majistare a Kano ta bayar da belin wata mata mai suna Amina Adamu da ake zargi da cin zarafin jami’an gwamnati a Kano
- Ana zargin matar da cizon wani ɗan sanda da kuma yaga rigar wani lauya yayin da suke gudanar da aikinsu a cikin kotun
- Amina ta musanta zarge-zargen da ake yi mata, yayin da kotu ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 25 ga Nuwambar shekarar 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wata kotun majistare da ke yankin Norman’s Land a cikin birnin Kano ta bayar da belin wata mata da ke zargin da cin zarafi.
Matar mai suna Amina Adamu, ana zarginta da cizon ɗan sanda da kuma yaga rigar wani lauya.

Source: Original
’Yan sanda sun gurfanar da Amina a gaban kotun bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da cin zarafin jami’an gwamnati da kuma hana ma’aikatan gwamnati gudanar da ayyukansu na bisa doka, cewar Daily Trust.
An wanke wani kan zargin kashe matarsa
Wannan na zuwa ne bayan wata kotu ta yi hukunci game da zargin wani mutum da kashe matarsa a jihar Kano.
Babbar Kotun Jihar Kano ta wanke wani mutum mai suna Tusuf Nadabo Kawule daga zargin da ake yi masa na kashe matarsa bayan shekary biyar ana shari'a.
Mai shari’a Nasir Saminu ya ce masu gabatar da ƙara sun kasa gabatar da isassun hujjoji don tabbatar da zargin.
Lamarin ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar hukumar Takai ta jihar Kano da ke yankin Arewacin Najeriya.
Bayan duba bayanan da aka gabatar a gaban kotu, Mai shari’a Saminu ya bayyana cewa hujjojin masu gabatar da ƙara ba su wadatar wajen tabbatar da zargin kisan kai ba.

Source: Facebook
Tuhume-tuhumen da ake yi wa Amina
Mai gabatar da ƙara, Barrister Khadija M. Madaki, ta buƙaci kotun da a karanta wa wadda ake tuhuma laifukan da ake zarginta da aikatawa.
Magatakardan kotun, Auwal Dauda, ya karanta mata tuhume-tuhumen, inda matar ta musanta aikata laifukan da ake zarginta da su domin kare kanta a kotun.
Har ila yau, mai gabatar da ƙarar ta roƙi kotun da ta ɗage sauraron shari’ar domin bai wa ɓangaren masu ƙara damar gabatar da shaidunsu.
Alƙalin kotun ya amince da buƙatar tare da ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar, cewar Punch.
Mata ta kashe ƴaƴan kishiyarta a Kano
Mun ba ku labarin cewa ’yan sandan sun kama mata mai shekara 20 da wasu mutum uku bisa zargin sacewa da kashe wani yaro mai shekara 14.
Yan sandan sun ce matar ta kitsa kashe ’ya’yan kishiyarta hudu domin danta tilo shi kadai ya gaji dukiyar mahaifinsu a nan gaba saboda son abin duniya.
An gano cewa matar ta dauki nauyin kisan ne duk da cewa mijinta, wanda shi ne mahaifin yaran, yana raye bai riga ya mutu ba.
Asali: Legit.ng

