Zaben 2027: Dan Takarar Shugaban Kasa ya Bayyana Sharadin Janyewa Daga Takara ga Su Atiku
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ce a shirye yake ya janye daga takara domin wani dan adawa ya maye gurbinsa a zaben 2027
- Adebayo ya gindaya sharadin shiga duk wata hadakar jam'iyyun adawa a wata hira da aka wallafa ranar 18 ga Oktoba, 2026
- Dan takarar ya bambanta hadakar da aka gina kan magance matsalolin kasa da wadda aka kafa kawai domin adawa da Shugaba Bola Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Shugaban sashen Hausa na Legit.ng, Salisu Ibrahim, yana da gogewar sama da shekaru shida wajen kawo rahotannin siyasa, zabe, harkokin jama'a da shugabanci a Najeriya da Afirka.
FCT, Abuja - Adewole Adebayo, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP a zaben 2027, ya ce yana shirye ya janye daga takara domin wani dan adawa, amma bisa sharadin cewa an gina hadakar ne kan kawo karshen talauci da rashin tsaro a Najeriya.
Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar The Punch ta wallafa ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026, lokacin da aka tambaye shi ko zai amince ya shiga tsarin zaben dan takarar hadin gwiwar 'yan adawa cikin gaskiya da adalci tare da mutunta sakamakonsa.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Yadda Tinubu, Atiku da Peter Obi ke fafatawar neman nasara a jihohin Arewa 5

Source: Twitter
Sharadin Adebayo na janyewa
Dan takarar na SDP ya bayyana cewa babban abin da yake damunsa ba wai janyewa daga takara ba ne. A cewarsa, abin da ya fi muhimmanci shi ne ko jam'iyyun adawa za su iya cimma matsaya kan tsarin magance manyan matsalolin Najeriya maimakon hada kai kawai domin adawa da Shugaba Bola Tinubu.
Adebayo ya ce:
"Ba na adawa da janyewa daga takara domin wani dan takara. Abin da nake magana a kai ba batun janyewa ba ne. Batun shi ne dukkan 'yan Najeriya su amince cewa dole ne mu kawo karshen talauci da rashin tsaro ta hanyar wannan zabe."
Ya yi ikirarin cewa dole ne a samar da gagarumin tushe na manufofi da za su hada kan 'yan adawa kafin hadakar ta zama mai ma'ana.
Ya kuma yi gargadin cewa hada kai kawai saboda rashin son shugaban kasa ba zai samar wa 'yan Najeriya manufa guda da za su yi aiki a kai ba.
Ya ce:
"Abin da zai hada kan 'yan adawa ya kamata ya zama abin da zai iya hada kan 'yan Najeriya ma. Ma'anar adawa da muke da ita ta yi fadi fiye da kima. Muna bukatar wani abu na zahiri da za mu hada kai a kansa."
Ya soki adawar Tinubu kawai
Dan takarar shugaban kasar na SDP ya kuma bayyana irin hadakar da ba zai amince ya shiga ba.
Ya ce ba shi da sha'awar shiga hadakar da aka kafa bisa kiyayya ko gaba da shugaban kasa, amma a shirye yake ya ba da gudummawarsa ga wadda aka gina kan cimma manufofin da za su amfani al'umma.
Adebayo ya ce:
"Amma idan kawai hadakar adawa ce ta masu kin Tinubu, ku cire ni a ciki. Ba na kin kowa har haka. Amma idan batun kawar da talauci da rashin tsaro ne, zan kasance cikinta."
Ya kara da cewa idan aka gina hadakar bisa irin wannan tsari, babu wata sadaukarwa ta siyasa da za ta gagare shi.
A cewarsa:
"A karkashin wannan tsari, babu wani abu mai tsada da ba zan sadaukar ba, matukar na gamsu cewa hakan zai taimaka wajen kawo karshen talauci da rashin tsaro a Najeriya."
Hasashen fafatawar su Atiku, Obi da Tinubu a zabe mai zuwa
A wani labarin, wani sabon nazari da wata jaridar Najeriya ta gudanar ya duba yanayin siyasa a jihohi biyar da suka hada da Kano, Adamawa, Bauchi, Benue da Kwara, yayin da ake fara shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.
Rahoton da jaridar The Nation ta wallafa ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026, ya yi nazari kan yadda tsarin jam'iyyu, sauya sheka da tasirin manyan 'yan siyasa za su iya shafar yadda masu zabe za su kada kuri'a a kowace jiha.
Shugaba Bola Tinubu na jam'iyyar APC, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyyar ADC da Peter Obi na jam'iyyar NDC na daga cikin manyan 'yan siyasar da ke shirin fafatawa a zaben.
Asali: Legit.ng

