Rawa da Shugabannin APC Ke Yi a Kamfen Ya Fara Damun Ƴan Najeriya

Rawa da Shugabannin APC Ke Yi a Kamfen Ya Fara Damun Ƴan Najeriya

  • Jam’iyyar PDP a Jigawa ta zargi shugabannin APC da nuna halin ko-in-kula ta hanyar rawa a wajen gangamin yaƙin neman zaɓe
  • Shugaban PDP na jihar, Babandi Gumel, ya ce al’umma na fama da yunwa, rashin aikin yi da tsadar kayan abinci
  • Sai dai APC ta kare rawar da shugabanninta ke yi, tana mai cewa hakan na nuna farin ciki da irin tarbar da suke samu daga jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Jam’iyyar PDP da APC a jihar Jigawa sun yi musayar kalamai kan rawar da shugabannin jam’iyyar APC ke yi a wajen gangamin yaƙin neman zaɓe.

Yayin da PDP ta bayyana hakan a matsayin rashin tausayi ga al’ummar da ke fama da matsin tattalin arziki, APC ta ce rawa da shagali na nuna farin ciki da kuma yadda jama’a ke karɓar shugabanninta.

Kara karanta wannan

Siyasa ba da gaba ba; Tawagar PDP ta ziyarci kusoshin APC da suka yi hatsari a Gombe

APC da PDP sun kaure da fada a Jigawa
Dandazon magoya bayan APC da ba PDP a Najeriya. Hoto: Peoples Democratic Party, PDP, All Progressives Congress.
Source: Twitter

Shugaban PDP na jihar Jigawa, Babandi Gumel, ne ya fara sukar shugabannin APC yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a birnin Dutse, babban birnin jihar, cewar Punch.

PDP ta caccaki shugabannin APC kan rawa

Gumel ya bayyana takaicinsa kan yadda shugabannin APC da manyan jami’an gwamnati ke rawa a wajen gangamin siyasa, alhali jama’a na fama da yunwa.

A cewarsa, abin kunya ne shugabannin jam’iyyar mai mulki su riƙa rawa a kan dandamalin siyasa yayin da al'umma ke cikin mawuyacin hali.

Ya ce:

"Abin kunya ne shugabannin APC su riƙa rawa a wajen gangamin yaƙin neman zaɓe yayin da talakawa ke shan wahala.
"Mutanenmu na fama da yunwa, matasanmu ba su da aikin yi, amma shugabannin APC suna ta rawa kamar komai yana tafiya daidai.
"Halin da ake ciki a zahiri yana da raɗaɗi. Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi, talauci ya mamaye ko'ina, amma shugabannin APC suna rawa, ku daina rawa, ku saurari kukan jama'a. Jagoranci ba rawa ba ne, jagoranci hidimtawa al'umma ne."

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Ana rigima tsakanin PDP da APC a Jigawa
Taswirar jihar Jigawa da APC ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

APC ta mayar da martani ga PDP

Sai dai sakataren yaɗa labaran APC a jihar Jigawa, Bashir Kundu, ya yi watsi da sukar da jam'iyyar PDP ta yi, inda ya bayyana rawa a wajen gangamin siyasa a matsayin nuna farin ciki ba wai rashin damuwa da halin da jama'a ke ciki ba.

Kundu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da wakilin jaridar PUNCH ya tuntube shi domin jin martaninsa kan zargin da PDP ta yi, cewar Vanguard.

Ya ce:

"Alhamdulillahi, dangane da tambayarka kan rawa ko dariya a lokacin gangamin siyasa, ina so ka fahimci cewa ba wani sabon abu ba ne.
"Halin ɗan Adam ne ya nuna farin ciki da jin daɗi idan ya tsinci kansa a cikin wani abu da yake faranta masa rai."

Kundu ya ce shugabannin APC da magoya bayanta na rawa ne saboda irin tarbar da suke samu daga mazauna jihar yayin rangadin yaƙin neman zaɓe.

Kara karanta wannan

Shinkafa da wake: An kafa kwamitin kamfen Tinubu da APC cike da yan adawa

Ya danganta irin wannan tarba da salon jagorancin Gwamna Umar Namadi da sauran shugabannin APC, waɗanda ya bayyana a matsayin masu tawali'u da kyautata mu'amala.

Mai magana da yawun APC ya kuma zargi 'yan adawa da nuna rashin jin daɗi saboda yadda jam'iyyar ke samun karɓuwa daga al'ummar jihar yayin gangamin yaƙin neman zaɓe.

Da aka tambaye shi ko ya dace shugabannin jam'iyyar su riƙa rawa a lokacin da wasu sassan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro, Kundu ya ce jihar Jigawa ba ta cikin halin jimami ko kuma fuskantar matsalar tsaro.

Sai dai ya ce APC na addu'ar Allah Ya kare jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro, tare da kawo musu sauƙi.

Ya ƙara da cewa:

"Amma duk da haka, hakan ba yana nufin mutum ba zai iya nuna farin cikinsa kan abin da yake faranta masa rai ba saboda wani yana cikin wani hali na daban.

Sule Lamido ya magantu kan siyasar 2027

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce rashin hadin kan Atiku Abubakar da Peter Obi yana kara wa Shugaba Bola Tinubu damar lashe zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Ba mu yi': APC ta gano masu saka ƴan daba su yi wa Tinubu rashin kunya

Lamido ya bayyana cewa da Atiku da Obi sun hada kai, da za su fi samun karfin kalubalantar Tinubu, inda ya ba da shawarar cewa Atiku ya zama dan takarar shugaban kasa.

Ya kuma yi gargadin cewa ko wane daga cikin manyan 'yan takarar ya lashe zaben, Najeriya ba ta da riba idan aka ci gaba da fifita burin siyasa kan hadin kan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.