Fashola Ya Fito da Bayanin da Ya Kamata Mutane Su Sani kan Yanayin Lafiyar Tinubu

Fashola Ya Fito da Bayanin da Ya Kamata Mutane Su Sani kan Yanayin Lafiyar Tinubu

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya ce bai ga wani abu da ke nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da lafiya ba
  • Fashola ya bayyana cewa duk da tsufan Tinubu, hakan ba yana nufin hankalinsa ya ragu ba, domin har yanzu yana gudanar da ayyukansa
  • Ya ce shugaban ya ƙara samun ƙwarewa a tsawon shekaru, yana mai cewa har yanzu yana da ƙarfin ɗaukar nauyin ayyuka masu wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan lafiyar jikin Shugaba Bola Tinubu da kuma ƙarfinsa na tunani.

Fashola ya ce bai ga wani abu da ke nuna cewa shugaban kasar ba zai iya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ba.

Fashola.
Tsohon gwamnan jihar Legas kuma tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola Hoto: Babatunde Fashola
Source: Facebook

Fashola, wanda ya riƙe muƙamin ministan ayyuka da gidaje a mulkin Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today.

Tinubu na da lafiyar jagorantar Najeriya?

An tambaye shi ko yana ganin Tinubu yana da ƙoshin lafiyar da zai iya jagorantar ƙasar, ya bda amsa da cewa:

“Babu wani abu da ya nuna min cewa bai da lafiya ko bai cancanci gudanar da wannan aiki ba. Eh, ya tsufa amma hakan ba yana nufin hankalinsa ya gushe ba.
"Har yanzu yana bayar da umarni, idan na gan shi, yana aiki, har yanzu yana karatu, yana amincewa da takardu tare da rubuta bayanai a kansu.”

Tun bayan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ake ci gaba tattaunawa a bainar jama'a kan lafiyar Tinubu da yanayin jikinsa.

Damuwar ta sake kunno kai a 2026, yayin da aka ƙara sanya ido kan yanayin shugaban a bainar jama'a, musamman bayan yaɗa wasu bidiyoyi a intanet da suka nuna yana tafiya a hankali a wasu taruka.

Sai dai fadar shugaban ƙasa da jam'iyyar APC sun sha kare shugaba Tinubu, suna mai cewa yana da ikon sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa.

Fashola ya ce Tinubu ya kara kwarewa

Tsohon gwamnan, wanda ya yi aiki kafada da kafada da Tinubu a lokacin da yake muqlkin jihar Legas na tsawon shekaru takwas, daga 2007 zuwa 2015, ya ce shugaban ya ƙara ƙwarewa a tsawon shekaru.

Da aka tambaye shi ya kwatanta Tinubu da ya sani a farkon shekarun 2000 da wanda yake shugabancin ƙasar a yanzu, Fashola ya ce mai girma Tinubu ya fi yadda yake a da.

Ya ce:

“Tabbas, yanzu ya fi wayewa da kwarewa, babu shakka a kan haka. Ni nan da kuke gani ba shugaban ma'aikatan da ya ɗauka a 2002 ba ne, shekaru 39 kenan da suka wuce.
"A lokacin ina da shekara 39, yanzu kuma ina da shekara 63. Don haka, dole ne mu yaba masa kan ƙwarewar da ya samu."

Jawaban Fashola sun ƙara shiga cikin jerin martanin da wasu abokan siyasar Tinubu ke bayarwa domin kare shugaban daga tambayoyi kan lafiyarsa da kuma ƙarfinsa na jagorantar ƙasa.

Kun ji cewa tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai yi alkawarin samar da wutar lantarki na awa 24 a Najeriya ba.

Fashola ya ce ya kamata 'yan Najeriya su tantance ayyukan gwamnatin Tinubu a bangaren wutar lantarki bisa irin ci gaban da suka gani a yankunansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262