Meye Gaskiyar Bidiyon da Aka Gano Sanusi II a Taron Ƴarsa da Ya Jawo Magana?

Meye Gaskiyar Bidiyon da Aka Gano Sanusi II a Taron Ƴarsa da Ya Jawo Magana?

  • Wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna ana zargin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya halarci bikin baje kolin kayan mata da ’yarsa ta shirya
  • Sai dai bincike ya gano cewa Sanusi ya halarci buɗe bikin ne kawai, inda ya yi addu’a tare da yanke katin buɗe taron
  • Binciken ya tabbatar da cewa babu wata shaida da ke nuna Sarkin ya halarci lokacin da mata suka fara baje kolin kayayyakinsu a wajen taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - An yi ta yaɗa wani bidiyo da ya jawo maganganu wanda aka gano Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a wurin wani taro da bai dace ba.

Bidiyon da ya yaɗu a kafafen sada zumunta da ke nuna ana zargin Muhammadu Sanusi II, ya halarci taron baje kolin kayan sawa da ’yarsa, Sabeera Sanusi, ta shirya a jihar Kano ya jawo ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

'Maganar yunwa fa ruruta ta ake yi': Jigon APC ya magantu kan halin kunci

An ƙaryata bidiyon da aka hango Sanusi II a taro
Sarki Muhammadu Sanusi II na jihar Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Facebook

Bidiyon Sarki Sanusi da ake yadawa

Bidiyon da wani mai amfani da kafar X mai suna @xagreat ya wallafa, ya nuna ana zargin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya halarci bikin The Royale Fair, wanda ’yarsa ta shirya.

Mai wallafa bidiyon ya rubuta cewa:

“Wane irin Sarki ne wannan? Ganduje ya yi daidai da korar wannan mutumin.”

Sai dai binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar kan bidiyon ya gano cewa babu wata shaida da ke tabbatar da cewa Sarkin ya halarci lokacin da ake nuna kayan sawa a wajen taron.

Abin da binciken ya gano

Binciken ya nuna cewa Sanusi II ya bayyana a wani bidiyo daban da aka wallafa a shafin sada zumunta na ’yarsa, inda ya halarci bikin buɗe taron.

A yayin bikin buɗewar, Sarkin ya yi addu’a tare da shiga cikin yanke kaset ɗin buɗe taron a hukumance.

Kara karanta wannan

Bidiyon da aka nuna Sarki Sanusi II da wasu 'yan mata ya jawo rudani

Sai dai ba a gan shi a sauran sassan bidiyon da ke nuna mata suna baje kolin kayayyakinsu da kuma nuna tufafin da suka samar ba.

Haka kuma, ƙarin binciken wasu bidiyoyi daga wajen taron ya nuna yadda mata suka gudanar da baje kolin kayayyakinsu, amma babu wata shaida da ta nuna cewa Sarkin ya kasance a wajen a lokacin.

An karyata halartar Sanusi II taron baje koli
Taswirar jihar Kano da Sarki Sanusi II ke sarauta. Hoto: Legit.
Source: Original

Hukuncin binciken gaskiya

Binciken ya tabbatar da cewa Muhammadu Sanusi II ya halarci bikin buɗe The Royale Fair, amma bai tabbatar da cewa ya kalli yadda matan suka gudanar da baje kolin kayan sawa ba.

Saboda haka, majiyoyi sun bayyana ikirarin da ake yaɗawa a matsayin mai ruɗarwa, domin bidiyon da aka tantance bai tabbatar da cewa Sarkin ya halarci lokacin baje kolin kayan matan ba.

Sarki Sanusi II ya bude masallaci

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya karbi bakuncin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda ya jagoranci bude Masallacin Zawiyya da aka sabunta a Gusau, babban birnin jihar.

Babban limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, shi ma ya halarci taron, inda ya jagoranci sallar Juma'a a masallacin mai dimbin tarihi.

Wasu masu amfani da Facebook sun yaba da aikin sabunta masallacin, yayin da wasu suka yi amfani da damar wajen sukar gwamnatin Zamfara kan matsalar tsaro da ke addabar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.