An Rage Mugun Iri: Manyan Kwamandoji da Hatsabiban 'Yan Ta'adda Sun Bakunci Lahira
- Hare-haren sama da rundunar Operation Hadin Kai ta kai sun hallaka mayakan ISWAP 21, ciki har da manyan kwamandoji, tare da jikkata wasu 10
- Sojojin sun kai hare-haren ne a Monguno da yankin Kudancin Tafkin Chadi tsakanin 16 zuwa 17 ga Nuwamba, 2026
- Rundunar ta kuma ce ta tarwatsa masana'antar kera bama-bamai ta ISWAP tare da kashe wani fitaccen ƙwararre kan bama-bamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno, Nigeria - Hare-haren da rundunar sojojin sama ta Operation Hadin Kai (OPHK) ta kai sun yi wa ƙungiyar ISWAP babban lahani a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Jiragen sojojin sun kashe mayakanta 21, ciki har da manyan kwamandoji, tare da jikkata wasu 10 a wasu hare-hare daban-daban a Jihar Borno.

Source: Twitter
Rundunar sojojin ta tabbatar da wannan nasara a wata sanarwa da ta wallafa a Facebook, inda ta ce an gudanar da hare-haren ne tsakanin 16 zuwa 17 ga Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan
Mazan fama: Amurka ta yabawa sojojin Najeriya bayan gudanar da wani gagarumin aiki
Jiragen sojoji sun kai samame
Sojoji sun kai farmaki kan ’yan ta’addan a Monguno da yankin Kudancin Tafkin Chadi, sun tarwatsa hanyar ƙungiyar ta kera bama-bamai tare da kashe wani muhimmin ƙwararre kan bama-bamai.
A harin farko, rahotannin sirri sun nuna cewa mayakan ISWAP na dosowa Monguno, lamarin da ya sa aka tura jirgin sama marar matuƙi (UAV) domin sa ido kan motsinsu.
Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Maiduguri.
Ya ce jirgin leƙen asirin ya gano yan ta'addan suna tafiya a daji a Arewa maso Gabashin Monguno, lamarin da ya kai ga kai musu hare-haren sama na musamman, inda aka kashe bakwai daga cikinsu.
Goni ya bayyana cewa Abba Bomma, wani muhimmin ƙwararre kan bama-baman IED, na cikin waɗanda harin ya kashe ko ya raunata har suka kasa ci gaba da yaƙi, yayin da wasu mayaka huɗu suka samu munanan raunuka.
An kashe manyan kwamandojin ISWAP
A wani harin daban da aka kai a Arinna, yankin Kudancin Tafkin Chadi, sojojin sun farmaki shugabanci da tsarin ayyukan ISWAP, inda suka kashe fitattun kwamandoji da wasu mayakanta.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai Mallam Sharki, wanda rundunar sojin ta bayyana a matsayin fitaccen mamba a majalisar shura ta ƙungiyar, kuma Amirul Amniya (Kwamandan Tsaron Cikin Gida).

Source: Original
An kuma kashe kwamandan mai suna Abu Saad, wanda aka bayyana a matsayin Qaid na Sabon Tumbu, tare da wasu mayaka 12. Wasu ƙarin mayaka biyar kuma sun samu munanan raunuka.
Rundunar soji ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da matsa wa ƙungiyoyin ta’addanci lamba har sai an dawo da zaman lafiya da harkokin yau da kullum a yankin Arewa maso Gabas.
Jiragen yaki sun kashe yan ta'adda 40
Kun ji cewa hare-haren jiragen yakin sojojin Najeriya sun hallaka mayakan kungiyar ISWAP 40 a yankin Wulgo–Momaduru da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno.
Zagazola Makama ya rawaito cewa majiyoyin tsaro sun ce harin farko da jiragen yakin suka kai ya hallaka mayakan ISWAP kusan 30 tare da lalata babur guda.
Asali: Legit.ng
