Amaechi Ya Jero Jihohin Ya Ce Tabbas Atiku zai Lashe Su a 2027
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar zai iya lashe jihohin Arewa 13 a zaɓen 2027
- Amaechi ya ce Shugaba Bola Tinubu na da damar samun nasara a jihohi biyar kacal na Kudu maso Yamma, yayin da APM za ta iya karɓar jihar Oyo
- Tsohon ministan sufuri ya bayyana cewa ADC za ta fafata da APC a yankunan Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya domin neman rinjaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya yi ikirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na da damar lashe jihohin Arewa 13 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Amaechi, wanda shi ne mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar a Bauchi.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto cewa tsohon ministan sufuri ya kwatanta ƙarfin siyasar Atiku da na Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce ADC na da kyakkyawar damar kayar da APC a wasu yankunan ƙasar.
Jihohin Atiku zai iya lashewa
Amaechi ya yi ikirarin cewa Atiku na da damar lashe dukkan jihohi 13 na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Ya kuma bayyana cewa Atiku zai iya samun nasara cikin sauƙi a jihohin Neja, Kogi da Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya.
A cewarsa, ADC za ta kuma fafata da APC a yankin Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya domin tabbatar da nasarar Atiku.
Jihohin da Tinubu zai lashe
Tsohon gwamnan ya ce Tinubu na iya samun nasara a jihohi biyar kacal cikin shida na Kudu maso Yamma, yankin da ya fito.
Ya yi hasashen cewa jam’iyyar APM za ta lashe jihar Oyo, yana mai cewa gwamnan jihar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, zai yi nasara a yankin.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027

Source: Facebook
Amaechi ya kuma bayyana cewa Kudu maso Gabas ba yankin da Tinubu zai iya samun gagarumar nasara ba, yana mai cewa ADC na da damar karɓar yankin.
Da yake jawabi a gangamin, Amaechi ya ce:
“Tinubu na da jihohi biyar kacal a Kudu maso Yamma, yayin da ta shida za ta koma hannun APM. Za mu fafata da shi a Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya.
“A Arewa ta Tsakiya, Atiku zai lashe Neja, Kogi da Nasarawa cikin sauƙi. Kudu maso Gabas ba yankin Tinubu ba ne. Ku kasance da tabbacin cewa ADC za ta yi nasara.”
Ga bayanin da Amaechi ya yi a kasa:
Ana hasashen nasarar Atiku
A wani labarin, kun ji cewa matakin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 na ci gaba da jan hankali.
Haka kuma, ana samun ikirarin cewa wasu magoya bayan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na sauya sheƙa, yayin da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ke ƙara jawo fushin jama’a.
Atiku ya ƙara mayar da hankali wajen jawo hankalin masu zaɓe a Arewa, inda ya buƙaci magoya bayansa a Sakoto su wayar da kan iyalansu da al’ummominsu, su fito ƙuri’a da yawa tare da kare ƙuri’unsu a zaɓen da ke tafe.
Asali: Legit.ng
