Har Yanzu Atiku na cikin Jerin Yan Takarar Shugaban Kasa a Shafin INEC? Bincike Ya Gano Gaskiya
- Hukumar INEC ba ta cire sunan Atiku Abubakar, daga matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a zaɓen 2027 ba
- Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, na nan a jerin sunayen a matsayin abokin takararsa
- Rikicin shugabancin ADC ya ƙara ƙamari yayin da ɓangarorin da ke takun saƙa ke neman hukumar zaɓe ta amince da su bisa hukuncin kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) cire sunan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar daga jerin yan takara a zaben 2027 ba.
Legit Hausa ta fahimci cewa har yanzu INEC na rike da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a jerin sunayen 'yan takarar zaɓen shugaban ƙasa na karshe da ta wallafa.

Source: Facebook
Binciken da Leadership ta yi a shafin intanet na INEC ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2027 ya nuna cewa har yanzu Atiku da abokin takararsa, tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, na cikin jerin sunayen ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Wannan lamari ya faru ne yayin da rikicin shugabancin jam'iyyar adawar ke ci gaba da ɗaukar sabon salo, bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 5 ga Nuwamba.
Kotun ta soke samuwar kwamitin gudanarwa na ƙasa da David Mark ke jagoranta, tare da rushe matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da tsarin da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC
Jam'iyyar ADC ta ɗaukaka kara
Sai dai ADC ta ƙalubalanci hukuncin a Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda ta shigar da ƙara mai dalilai 17 tare da neman hana INEC sauya bayanan shugabancin jam'iyyar ko bayanan takarar 'yan takararta na shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi.
ADC ta yi zargin cewa aiwatar da hukuncin kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci zai iya jefa takardun tsayawar 'yan takararta cikin matsala.
Nafiu Bala ya tura sako g INEC
Nafiu Bala ya kuma rubuta wa INEC wasiƙa domin sanar da hukumar cewa ya koma kan muƙaminsa na shugaban ADC na ƙasa, bisa bin umarnin hukuncin kotun na ranar 5 ga Nuwamba.
Ya kuma haɗa da sahihin kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da ingancinsa a matsayin wani ɓangare na wasiƙar.
Matsayar INEC ta jawo hankali
Ganin sunayen Atiku da Amaechi a jerin sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa na ƙarshe, har zuwa ranar 17 ga Nuwamba, ya sake jawo hankalin jama'a kan matsayar INEC game da iƙirarin ɓangarorin biyu.
Ana sa ran martanin hukumar INEC kan wasiƙar Nafiu Bala da kuma ƙarar da ke gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara zai taka muhimmiyar rawa wajen fayyace inda rikicin zai nufa a gaba.
ADC da dage kan takarar Atiku
Kun ji cewa ADC ta dage cewa Atiku Abubakar zai kasance cikin ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da hukuncin kotu da ya soke takararsa
Jam’iyyar ta kuma yi iƙirarin cewa Atiku zai samu gagarumar nasara a zaɓen, duk da ƙalubalen shari’a da ya dabaibaye shugabancinta da shirye-shiryenta na zaɓen mai zuwa.
Asali: Legit.ng

