"Ba Zai Yiwu Mu Koma Baya ba," Gwamna Ya Yi Fatali da Yunkurin Dawo da Tallafin Fetur

"Ba Zai Yiwu Mu Koma Baya ba," Gwamna Ya Yi Fatali da Yunkurin Dawo da Tallafin Fetur

  • Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya ce Najeriya ba za ta iya sake dawo da tallafin man fetur ba, yana mai gargaɗin cewa hakan zai ƙara talauci tare
  • Mbah ya kare matakin cire tallafin, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta tabbatar ’yan Najeriya sun amfana da kuɗaɗen da aka samu
  • Gwamna Mbah ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙarfafa masu zuba jari su ƙara saka kuɗaɗensu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu, Nigeria - Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya ce Najeriya ba za ta iya sake dawo da tallafin man fetur ba, yana mai gargaɗin cewa hakan zai ƙara jefa mutane cikin kangin talauci.

Gwamna Mbah ya ce dawo da tallafin zai iya dakile yunkurin yan kasuwa daga kasashen duniya da ke da niyyar zuba jarinsu a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Kai ne Masar," Atiku ya maida martani bayan Tinubu ya yi misali da tarihin Annabi Musa AS

Peter Mbah.
Gwamnan jihar Abia, Peter Mbah a gidan gwamnatinsa yayin taron Majalisar zartarwa ta jiha Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa Mbah ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron tattaunawa da ’yan takarar siyasa mai taken Meet the Candidates, inda ya kare matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin fetur.

Mbah ya soki maganar dawo da tallafi

Ya bayyana kiraye-kirayen sake dawo da tallafin a matsayin rashin fahimtar halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, yana mai cewa abin da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali shi ne tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun amfana da manufar.

“Idan kuka sake dawo da tallafin man fetur a yau, za mu yi asarar ninki 10 na duk abin da muke ƙoƙarin samu ta hanyar cire tallafin. Talaucin da da za mu fuskanta zai yi tsanani sosai, domin darajar Naira za ta ragu.
“Ba za mu iya komawa ga tsarin tallafin man fetur ba. Kuma ban ga amfanin mu dawo muna yin muhawara a kan wannan batu ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi misali da Annabi Musa kan batun dawo da tallafin fetur

“Bai kamata ma mu yi muhawara a kansa ba, domin ba ma son mu aika wa masu shirin zuba jari saƙon cewa muna tunanin sake dawo da tallafin. Hakan zai mayar da mu baya, ya haifar da firgici a tsarin tattalin arziki tare da sa masu zuba jari ja da baya.

- Gwamna Peter Mbah.

Ya buƙaci jawo masu zuba jari

Mbah ya buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙarfafa masu zuba jari su ƙara saka kuɗaɗensu a Najeriya, inda ya nuna ci gaban da aka samu a kasuwar hannayen jari a matsayin alamar ƙaruwa da amincewar masu zuba jari.

Peter Mbah.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah lokacin da ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce manufofin Tinubu sun taimaka wajen daidaita muhimman alamomin tattalin arziki tare da ƙarfafa zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa ana sa ran wannan yanayi zai ƙara ƙarfi saboda muhimman alamomin samun tattalin arziki a Najeriya sun inganta, cewar rahoton Punch.

Gwamna Mbah ya yi sababbin nade-nade

Kun ji cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya amince da naɗin sababbin hadimai 101 da suka haɗa da masu ba shi shawara da manyan mataimaka.

Sababbin naɗin sun ƙunshi masu ba da shawara na musamman bakwai, manyan mataimaka shida da mataimaka na musamman 88.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262