An Samu Daidaito, Gwamnatin Tinubu Za Ta Suburbuɗo wa Ma'aikata N70,000 duk Wata

An Samu Daidaito, Gwamnatin Tinubu Za Ta Suburbuɗo wa Ma'aikata N70,000 duk Wata

  • Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun sasanta rikicin da ya shiga tsakaninsu kan alawus ɗin sufuri na N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi
  • Shugabannin ƙungiyoyin biyu sun cimma matsayar yin aiki tare cikin mutunta juna da haɗin kai domin kare haƙƙoƙin ma’aikata da waɗanda suka yi ritaya
  • Tsofaffin shugabannin NLC da TUC sun shiga tsakani wajen sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Joe Ajaero da Festus Osifo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya (NLC) da na TUC sun sasanta rikicin da ya shiga tsakaninsu, inda suka amince su haɗa kai wajen kare muradun ma’aikata.

Shugabannin ƙungiyoyin biyu ne suka bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da suka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Kungiyoyin kwadago sun samu daidaito
Shugabannin kungiyoyin TUC da NLC yayin taro a Abuja. Hoto: Nigeria Labour Congress, HQ.
Source: Twitter

Sanarwar sulhun ta ƙunshi sa hannun shugaban NLC, Joe Ajaero, da takwaransa na TUC, Festus Osifo, tare da Hassan Sunmonu, wanda ya sanya hannu a madadin tsoffin shugabannin ƙungiyoyin, cewar Punch.

Yadda rikicin ya ɓarke tsakanin NLC da TUC

A watan Oktoba ne gwamnatin tarayya ta sanar da bayar da alawus ɗin sufuri na N70,000 ga ma’aikatan gwamnati na tsawon watanni shida.

Gwamnatin ta bayyana wannan matsaya ne a cikin yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka cimma bayan ganawa tsakanin wakilanta da shugabannin NLC a Abuja.

Sai dai bayan sa'o'i 24, TUC ta yi watsi da wannan alawus, tana mai cewa ya kamata gwamnati ta ƙara albashin ma'aikatan Najeriya maimakon bayar da tallafin sufuri na wucin gadi.

A martaninsa, Ajaero ya ce ya kamata TUC ta tattauna da gwamnatin tarayya domin cimma nata yarjejeniyar maimakon sukar sakamakon tattaunawar da NLC ta yi.

Osifo ya mayar da martani da cewa an fara tattaunawa kan alawus ɗin tun kafin ganawar Ajaero da gwamnati, yana mai cewa ita ma gwamnatin ta tattauna da TUC kan jin daɗin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Dangote ya dauki nauyin bikin baje kolin noma na 2026, abinci zai wadata a Arewa

Tinubu zai fara ba ma'aikata N70,000 duk wata
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tsofaffin shugabanni sun shiga tsakani

A sanarwar haɗin gwiwarsu, ƙungiyoyin sun bayyana cewa tsofaffin shugabannin NLC da TUC sun shiga tsakani domin sasanta rikicin da ya shiga tsakanin Ajaero da Osifo.

Sun ce sun amince baki ɗaya za su ci gaba da aiki tare cikin mutunta juna, amincewa da haɗin kai domin kare muradun ma'aikata, waɗanda suka yi ritaya da sauran masu rauni a cikin al'umma.

Sun ƙara da cewa haɗin kan ma'aikatan Najeriya ya fi duk wani saɓani da zai iya shiga tsakanin shugabannin ƙungiyoyinsu muhimmanci, cewar rahoton Vanguard.

Sanarwar ta ce:

“Babban gwagwarmayarmu, tarihin da muke da shi tare da alhakin kare haƙƙoƙin ma'aikata bai kamata a taɓa sadaukar da su saboda rashin fahimta ko bambancin ra'ayi tsakanin ƙungiyoyi ba.”

Ƙungiyoyin sun kuma jaddada cewa jin daɗi, mutunci da walwalar ma'aikata ba abubuwa ba ne da za a yi sassauci a kansu.

Yadda Tinubu ya ware N70,000 ga ma'aikata

Kara karanta wannan

Rusa takarar Atiku: Kalubalen da ke gaban ADC kan zaben 2027

A baya, an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da ba ma’aikatan gwamnati tallafin sufuri na N70,000 duk wata na tsawon watanni shida.

Gwamnati ta amince da biyan bashin wasu alawus-alawus na ma’aikata daga 1 ga Mayun 2026, cikin kashi uku daidai, daga Nuwamba.

Gwamnati da NLC sun kasa cimma matsaya kan ranar fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, amma sun amince da fara tattaunawa nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.