Wasu Shugabannin PDP Sun Yashe Sun Rabu da Su Pantami, Sun Shiga APC a Gombe

Wasu Shugabannin PDP Sun Yashe Sun Rabu da Su Pantami, Sun Shiga APC a Gombe

  • Shugabannin PDP na Kwami da Nafada a jihar Gombe, Idris Yayayi da Yusuf Jigawa, sun fice daga jam’iyyar zuwa APC
  • Wasu rahotanni sun ce shi ma shugaban PDP na karamar hukumar Yamaltu-Deba ya rabu da su Isa Ali Pantami a jihar Gombe
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da su, yana mai cewa shigowarsu za ta kara wa APC karfi gabanin zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Gombe - Shugabannin jam’iyyar PDP na wasu kananan hukumomin Gombe sun sauya-sheka zuwa APC mai mulki a jihar da Najeriya.

Shugabannin da wasu Mabiya sun dauki wannan mataki ne a lokacin da ake shirin zaben sabon gwamna a jihar Gombe a takarar 2023.

Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya lokacin annobar COVID-19 a Gombe Hoto: GovernorInuwa
Source: Twitter

Gombe: Shugabannin kananan hukumomin PDP sun bar ta

Daily Trust ta ce wadanda suka sauya shekar sun hada da Idris Abubakar Yayayi wanda shi ne shugaban PDP na karamar hukumar Kwami.

Kara karanta wannan

Shugaban jam’iyyar APC da aka yi garkuwa da shi a Kano ya tsira bayan kwanaki 68

Shi ma Alhaji Yusuf Isa Jigawa wanda yake shugaban PDP na ƙaramar hukumar Nafada ya bar ta.

Hakan yana nufin 'yan siyasar za su yi amfani da karfi da dabarunsu wajen tallata Bola Tinubu, Jamiliu Gwamna da sauran 'yan takaran APC.

Gwamnan Inuwa Yahaya ya gana da shugabannin PDP

Shugabannin biyu sun sanar da ficewarsu daga PDP ne bayan wasu tarurruka daban-daban da Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya.

Sanarwar sauya shekar ta fito daga bakin Darakta Janar na yada labarai a gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli a karshen makon jiya.

Ya ce Sanata Usman Bayero Nafada, wanda yana cikin manyan kwamitin yakin neman zaɓen APC a jihar, ne ya taimaka wajen jawo ‘yan siyasar.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar ya shirya zaman da aka yi tsakanin gwamnan da tsofaffin shugabannin PDP na kananan hukumomin jihar.

Ya bayyana cewa kafin sauya shekar, mutanen biyu sun mika takardun ajiye mukamansu da ficewa daga PDP ga shugabannin jam’iyyar na mazabunsu.

Kara karanta wannan

Matsaloli 10 da Sheikh Isa Pantami ya tsallake wajen zama ‘dan takarar gwamna a Gombe

‘Dan siyasar ya ce hakan ya kawo karshen kasancewarsu mambobin babbar jam’iyyar hamayyar.

Taimakon da za su ba APC a Gombe

Haka kuma, tsofaffin shugabannin sun yi alkawarin tattaro duk magoya bayansu, tsarin siyasarsu da hanyoyin yakin neman zaɓensu zuwa APC.

Za su yi bakin kokari domin karfafa APC a kananan hukumomin Kwami da Nafada a zaben badi.

The Guardian ta ce shugaban karamar hukumar Yamaltu-Deba, Hon. Adamu Alhaji Abdu yana cikin wadanda suka yi sallama da PDP ta reshen Gombe.

Sauran ‘yan siyasa kamar shugaban PDP a mazabar tsakiyar jihar Gombe: Hon. Babangida Usman da aka fi sani da Ventures sun shiga jirgin APC mai mulki.

Babangida shugaba ne a wani kwamiti na Pantami kafin ya zabi ya tsallaka daga jam'yyar adawar.

A yayin ganawarsu da gwamnan, sun yaba da irin jagorancin da yake yi tare da bayyana aniyarsu ta bayar da gudummawa wajen ba shi nasara.

Gwamna ya yi masu maraba da zuwa APC

Da yake maraba da su cikin APC, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa shigowarsu jam’iyyar za ta kara mata karfi sosai kuma su fadada tasirinta.

Kara karanta wannan

Wike ya tada wa gwamnonin APC 3 hankali da yan takaran da ya kawo jihohinsu

Gwamnan ya kuma bayyana fatansa na cewa gogewarsu a harkokin siyasa, tasirinsu da kwarewarsu wajen jawo magoya baya za su taimaka masu.

Sanarwar ta kara da cewa sauya shekar na nuna yadda tasirin shugabancin Gwamna Inuwa da APC ke karuwa a Gombe daf da zaben shekarar 2027.

Isa Pantami
Isa Pantami wanda yake takarar gwamna a PDP a Gombe Hoto: @ProfIsaPantami
Source: Twitter

Sanatan Gombe ya rabu da jam'iyyar PDP

A lokacin da Sheikh Isa Pantami ya sauya-sheka sai aka ji labari Sanata Bayero Nafada ya yi murabus daga jam'iyyar PDP a Jihar Gombe.

Wannan ya zama babban nakasu ga yunkurin takarar gwamnan malamin addinin Musuluncin bayan komawarsa jam'iyyar daga APC a watan Mayu.

An yi hasashen cewa Nafada zai koma APC bayan ganawa da Gwamna Inuwa Yahaya da sauran shugabannin jam'iyyar, kuma haka aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng