Siyasa: Bayero Nafada ya sake watsi da taron APC a jihar Gombe
- Babban sakataren Jam'iyyar APC, Alhaji Mai Mala Buni, ya kaddamar da manyan jami'an jam'iyya a jihar gombe don gudanar da harkokin jam'iyya na jihar, a karshen satin da ya gabata
- Jami'an daya gabatar sun hada Mista Nitte Amangal, shugaba; Gabani Ado, mataimakin shugaba; Adamu Abubakar, sakatare; da kuma Abayomi Williams, mai bada shawara
Sauran sun hada da Rose Danjuma (shugabar mata), Ibrahim Sabo (public relation officer), Kawu Mohammed Masu (shugaban matasa) da kuma Danladi Shu'aibu (ex-officio).
An kaddamar dasu ne saboda samo mafita akan matsalar da ake samu a cikin jam'iyyar tun a shekarar 2015.
Da yake jawabi jim kadan bayan gabatarwa, Buni ya yi kira ga 'yan jam'iyya dasu tallafawa sababbin jami'an don yin gwagwarmaya da jam'iyyar PDP a zaben 2019 mai zuwa
DUBA WANNAN: Janar Babangida ya kira shugaba Buhari ya bar wa yara a 2019
A bayanin da yayi, shugaban jam'iyyar na jiha, Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya godewa sakataren jam'iyyar na kasa, akan ceto jam'iyar ta APC da yayi a jihar Gombe.
Goje ya tabbatar da goyon bayan sa ga jam'iyyar kuma yayi kira ga dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC da su hada kai, domin ganin an samu nasarar zabe a shekara mai zuwa ta 2019.
"Mun sha wuya, kuma munyi aiki tukuru wurin ganin jam'iyyar nan ta kafu, saboda haka ina kira ga dukkanin masu son tsaya wa takarar gwamna da su ba da hadin kai, saboda baza mu yarda wani ya bata mana tafiyar mu ba har mu rasa kujerar gwamna ta 2019 a jihar Gombe," in ji Goje.
Sanata Usman Nafada da wasu daga cikin magoya bayan sa, wanda suka ki halartar taron da aka yi a baya na 21 ga watan Oktoban 2017, sun kara gujewa taron a wannan karon ma.
Manya - Manyan shugabannin APC da suka halarci taron sun hada Sanata Danjuma Goje, Bala Ibn Na'allah, Yunusa Ustaz da kuma Aishatu Dukku, Alhaji Inuwa Yahaya, tsohon dan takarar gwamna a 2015, tsohon ministan sufuri, Sanata Idris Abdullahi Umar, Alhaji Umar Farouk Bamusa, Alhaji Umaru Kwairanga da kuma wasu manya - manyan shugabannin jam'iyya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng