Gwamna Inuwa Yahaya Ya Ce Rufin Asirin Jama'a na cikin Nasarar APC a 2027

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Ce Rufin Asirin Jama'a na cikin Nasarar APC a 2027

  • Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe ya jaddada kira a zabi Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana haka ne yayin taro da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga karamar hukumar Akko a jihar Gombe
  • A bayanin da ya yi, gwamnan ya yaba wa mutanen karamar hukumar Akko kan yadda suke ba shi hadin kai wajen tafiyar da gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya karɓi babbar tawaga daga ƙaramar hukumar Akko a ziyarar nuna goyon baya.

Tawagar ta ƙunshi ‘yan majalisun tarayya da na jiha, manyan jiga-jigan jam’iyya, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da dimbin magoya bayan jam’iyyar APC.

Gwamna Inuwa Yahaya a Gombe
Lokacin da Inuwa Yahaya ke kira a zabi Bola Tinubu a Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a wani sako da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace daliban da suka je yin jarabawar JAMB

Gwamna Inuwa Yahaya ya bukaci a zabi APC

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi kira ga al'ummar da suka hadu a wajen taron da su marawa jam'iyyar APC baya a dukkan matakai, yana cewa nasarar jam'iyyar ce rufin asirin su.

A wani bidiyo da gwamnatin jihar ta wallafa a Facebook, gwamnan ya ce:

"A alamun da na gani, Na tabbatar kuna goyon APC, za mu yi zabe daga sama har kasa, mu kawo APC, shugabamu Bola Ahmed Tinubu ya dawo, 'yan majalisu da Sanatoci su dawo, gwamnan APC ya dawo, ciyamomi su dawo, kansiloli su dawo.
"To shi ne rufin asirin mu. in ku ka bari wani ya zo ya ɗaiɗaita mu, Allah ya kiyaye."

Magana kan zaben sanata a Gombe

Gwamna Inuwa Yahaya ya yaba da halin dattaku da hadin kai da kuma fahimtar juna da al’ummar Akko suka nuna wajen mara wa ‘yan uwansu na Yamaltu/Deba baya domin su samar da Sanata na gaba, maimakon Danjuma Goje.

Kara karanta wannan

Yadda APC ke fatan samun miliyoyin kuri'u a Kano da Katsina a zaben 2027

A bayanin da ya yi, ya ce za a isar da wannan matsaya da suka dauka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabancin jam’iyyar APC na ƙasa.

Mahalarta taron APC a Gombe
Inuwa Yahaya na yi wa 'yan APC daga Akko bayani a gidan gwamnatin Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Ya bayyana cewa lokutan zaɓe lokaci ne na tantance shugabanni, inda ya ce dole ne masu mukamai su nuna nagarta da biyayya ga jam’iyya domin sake samun amincewar jama’a.

Ya kuma danganta rashin nasarar APC a wasu sassan Gombe ta Tsakiya a zaɓen baya da ayyukan sanatan yankin wanda ya yi aikin da ya saba wa jam’iyyar.

Legit ta tattauna da Hamza

Wani dan jihar Gombe, Adamu Hamza, ya shidawa Legit cewa duk da yana tare da gwamna Inuwa Yahaya, amma ba lallai ya zabi Bola Tinubu ba.

Ya ce:

"Muna goyo bayan gwamnan ne saboda mun yarda da ayyukan da ya ke yi, amma shugaban kasa kuma gaskiya akwai damuwa.
"Saboda haka ba zai yiwu a ce zaben shi ya zama rufin asirin kowa da kowa ba."

An yi wa Tinubu addu'a a Yobe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Yobe ya tara malaman Musulunci domin su yi wa Najeriya, shugaba Bola Tinubu da sauran shugabanni addu'a.

Kara karanta wannan

Wutar rikici ta fara tashi a jam'iyyar APC, Yilwatda ya gargadi tsafaffin ƴan PDP

Mai Mala Buni ya bayyana cewa akwai bukatar yi wa kasa addu'a domin kare ta daga dukkan makircin da za a kulla mata daga ciki ko waje.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta ce malaman sun amince da yi wa shugaban kasar addu'a domin samun nasara a abubuwan da ya sa a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng