Sanata Yari Ya Ɗauko Da Zafi, Ya Kutsa Wata Jiha domin ba Tinubu Ɗaruruwan Ƙuri'u

Sanata Yari Ya Ɗauko Da Zafi, Ya Kutsa Wata Jiha domin ba Tinubu Ɗaruruwan Ƙuri'u

  • Abdulaziz Yari ya bukaci al’ummar Ekiti su bai wa Shugaba Bola Tinubu kuri’u 800,000 a zaben shugaban kasa na 2027
  • Tsohon gwamnan Zamfara ya ce Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu saboda ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a Ekiti
  • Yari ya bayyana cewa al’ummar Arewa za su goyi bayan Tinubu a 2027, yana mai cewa za su tabbatar masa da nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ekiti - Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Abdulaziz Yari, ya bukaci al’ummar jihar Ekiti su sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Yari, wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne, ya ce Tinubu ya yi kokari wajen gudanar da mulki, don haka ya cancanci samun wa’adi na biyu.

Yari ya nema wa Tinubu ƙuri'u a Ekiti
Sanata Abdulaziz Yari da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwambar 2026, yayin gangamin yakin neman zaben APC a jihar Ekiti, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Amaechi ya faɗi abin da zai sa ya rabu da matarsa saboda Tinubu

Yari ya nemi kuri’u 800,000 a Ekiti

A yayin jawabin nasa, Yari ya bukaci al’ummar jihar su tabbatar da samun akalla kuri’u 800,000 ga Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

Ya bayyana cewa adadin kuri’un ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kuri’un da ake sa ran za a kada a jihar.

Yari ya ce Tinubu bai manta da al’ummar Ekiti ba, inda ya lissafa wasu ayyukan da gwamnatin tarayya ta gudanar a bangaren ilimi, tituna da tallafawa matasa da mata.

Adadin masu katin zabe a Ekiti

Tsohon gwamnan ya tuna cewa a zaben shugaban kasa na 2023, jihar Ekiti ta bai wa Tinubu kashi 80 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Ya bukaci al’ummar jihar su kara yawan kuri’un da za su ba shugaban kasar a zaben 2027.

Yari ya bayyana cewa daga cikin masu rajistar zabe 1,080,000 a jihar, sama da 900,000 ne suka karbi katin zabe na dindindin (PVC).

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya tsallake Kogi zuwa Kano, yana neman kuri'u miliyan 2 ga Tinubu

Ya ce:

"A yau, cikin masu rajistar zabe 1,080,000, sama da 900,000 sun karbi katunansu na PVC. Ina son gabatar da bukata wadda ita ma bukatar shugaban kasa ce.
"Muna neman kuri’u 800,000, wanda yake wakiltar kusan kashi 90 cikin 100 na kuri’un da za a kada. Shi ya sa nake neman wannan kaso."
An nemawa Tinubu ƙuri'u a Ekiti
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Original

Yari ya magantu kan goyon bayan Tinubu a Arewa

A cewarsa, halartar tasu na nuna hadin kai da goyon baya ga gwamnan da kuma kudirin sake zaben Tinubu.

Yari ya bukaci shugabannin Ekiti su kara kaimi wajen wayar da kan al’umma, yana mai cewa Tinubu ya yi alkawarin kara ayyukan raya jihar idan aka sake zabensa.

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta rage hauhawar farashi da farashin kayan abinci da sama da kashi 50 cikin 100, cewar Daily Post.

Ya ce:

"Mu a Arewacin Najeriya muna daukar Bola Ahmed Tinubu a matsayin daya daga cikinmu, kamar yadda al’ummar Ekiti, Ondo, Oyo, Osun da Lagos suke yi."

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya fadi abubuwa 3 za su ba Tinubu nasara a zaben 2027

Yari ya bukaci al’ummar Ekiti su tabbatar ba a yi asarar kokarin gwamnatin Tinubu ba, yana mai cewa bai kamata a bar ayyukan shugaban kasar su tafi a banza ba.

Tsohon gwamna ya yi watsi da Tinubu

An ji cewa tsohon gwamnan Osun, Olagunsoye Oyinlola, ya janye goyon bayan da ya bai wa Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Oyinlola ya ce yarjejeniyar siyasar da ta sa ya goyi bayan Tinubu ta ƙare, saboda ba a cimma burin da ake son cimmawa ba.

Tsohon gwamnan ya buƙaci Tinubu da Atiku Abubakar su yi ritaya daga siyasa, su bar matasa su karɓi ragamar mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.