2027: Sanata Yari Ya Yanke Hukunci kan Wanda Ya Cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

2027: Sanata Yari Ya Yanke Hukunci kan Wanda Ya Cancanta tsakanin Tinubu, Atiku da Peter Obi

  • Abdulaziz Yari ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya kama kafar Shugaba Bola Tinubuwajen cancanta, ƙwarewa da nagarta
  • Sanatan ya nemi ’yan Jam’iyyar APC su yi aiki tukuru domin ganin Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Yari ya kuma bukaci magoya bayan APC su yi wa Tinubu da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, addu’ar samun nasara a zaɓensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu nagarta.

Sanata Yari ya ce duka yan takarar da ke ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba su kai shi cancanta da ƙwarewa ba.

Yari.
Sanata Abdulaziz Yari, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu na APC Hoto: Abdulaziz Yari
Source: Twitter

Yari, wanda ke wakiltar Mazabar Sanatan Zamfara ta Yamma a Majalisar dattawa ta 10 ya bayyana hakan ne ranar Laraba da ta wuce, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Daraktan kamfen Tinubu ya fadi haka ne a lokacin da yake jawabi ga tawagar Ƙungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Najeriya, NURTW, a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda ya nemi goyon bayansu ga sake zaɓen Tinubu.

Sanatan, wanda aka naɗa Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC a ranar 22 ga Agusta, ya ce yaƙin neman zaɓen zai wuce batun zaɓe, inda za a riƙa tattaunawa da ’yan Najeriya kan makomar ƙasar.

Sanata Yari ya dora yan takara a sikeli

Yari ya ce idan aka kwatanta sauran ’yan takarar shugaban ƙasa da Tinubu ta fuskar cancanta da ƙwarewa, babu wanda ya kai shi.

The Cable ya ruwaito Sanata Yari na cewa:

“Haka siyasa take. Idan ka ɗora dukkan ’yan takarar da ke fafatawa da Bola Ahmed Tinubu a kan sikeli, ina ganin sikelen ma ba zai karɓe su ba.
“Dukkanmu mun san cewa babu ɗaya daga cikin ’yan takarar da ke fafatawa da shi da ya kai shi a wajen cancanta da ƙwarewa; ba ma tunanin ko ɗaya daga cikinsu yana da ko da kashi 10 cikin 100 na nagartar Bola Tinubu.”

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya kamata ya sa 'yan Arewa su ki zabar Tinubu a 2027'

APC zs ta yi aiki tukuru kafin 2027

Yari ya amince cewa sauran ’yan takara suna da ’yancin tsayawa takara da gudanar da yaƙin neman zaɓe, amma ya ce APC za ta yi aiki tuƙuru domin ganin Tinubu ya samu nasara a 2027.

Yari da Tinubu.
Sanata Abdulaziz Yari tare da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya kuma bukaci magoya bayan APC su yi wa Tinubu da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, addu’ar samun nasara a zaɓensu daban-daban.

“Allah Ya ba su damar kammala kyakkyawan aikin da suka fara wa al’ummar ƙasar nan," in ji Yari.

Yari ya fadi yadda za su tallata Tinubu

Kun ji cewa Darakta janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya bayyana hanyar tallata Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana cewa cewa kamfen ɗinsa na zaɓen 2027 zai kasance kan batutuwa da nasarorin gwamnati, ba wai kai wa wasu mutane hari ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262