Babbar Magana: Amaechi Ya Faɗi Abin da Zai Sa Ya Rabu da Matarsa saboda Tinubu
- Rotimi Amaechi ya ce zai rabu da matarsa idan ta zama shugabar kasa ta yi mulki irin na Shugaba Bola Tinubu
- Tsohon gwamnan Rivers ya bukaci ’yan Najeriya su ajiye bambancin addini, siyasa da kabila wajen zaben shugaban kasa a 2027
- Amaechi ya bukaci ’yan Najeriya su ba ADC dama, tare da kare kuri’unsu daga magudin zabe a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana abin da zai iya yi wa matarsa musamman saboda irin salon mulkin Bola Tinubu.
Amaechi ya ce zai iya rabuwa da matarsa idan ta zama shugabar Najeriya kuma ta gudanar da mulki irin na Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Amaechi Ya shawarci yan Najeriya
Amaechi, wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Rapid TV da Punch ta bibiya.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya kuma magana, ya ba Tinubu shawarar da za ta taimaki gwamnatinsa
Amaechi ya bukaci ’yan Najeriya su manta da bambancin addini, siyasa da kabila wajen zaben 2027.
Tsohon gwamnan Rivers ya ce kusancin da ke tsakaninsa da matarsa ba zai hana shi sukar ta ba idan ta gudanar da mulki yadda Tinubu yake yi.
Ya ce:
“A yau, mutum mafi kusanci da ni a rayuwa ita ce matata, ba ’ya’yana ba. Don haka, idan gobe matata ta zama shugabar kasa kuma tana yin abin da Tinubu yake yi, zan yi kuskure idan na bi ta saboda soyayyar da ke tsakanina da ita. Ko dai ta canza, ko kuma in rabu da ita.”

Source: Facebook
Amaechi ya bukaci a watsar da Tinubu
Amaechi ya bukaci ’yan Najeriya su tantance irin ayyukan da shugaban kasa ya yi, maimakon barin alaka ta kashin kai ta rinjayi zabinsu na siyasa.
Ya ce:
“Ina sa ran ’yan Najeriya ba za su manta da addini, siyasa da kabila ba. Su yi watsi da Tinubu kawai.”
Dan takarar ADC ya ce ’yan Najeriya sun riga sun ga irin salon mulkin Tinubu, don haka ya kamata su ba jam’iyyar adawa dama a zaben 2027.
Ya kara da cewa:
“Akwai bambanci tsakanin tawagar Tinubu da tamu. An gwada su, don haka kun san cewa idan suka samu karin shekaru hudu, za ku mutu. Ba a gwada mu ba, saboda haka ku ba mu dama.”
Amaechi ya soki gwamnatin Tinubu
Tsohon ministan ya sake sukar gwamnatin Tinubu, inda ya yi amfani da ka’idar kwamfuta ta “Garbage in, garbage out”, wato idan aka shigar da bayanai marasa kyau, sakamakon da za a samu shi ma ba zai yi kyau ba.
Ya ce:
“Yanzu kun san cewa Tinubu ba shi da kyau. Idan kun san cewa Tinubu ba shi da kyau, kuma kuka shigar da abubuwa marasa kyau, wane sakamako kuke tsammani? Abin da zai fito shi ma zai zama mara kyau.”
Amaechi ya tuna rigimarsa da Obasanjo
Mun ba ku labarin cewa Rotimi Amaechi ya bayyana yadda barazanar kama shi da Obasanjo ya yi ta tilasta masa barin Najeriya zuwa Ghana.
Tsohon gwamnan ya ce ya ci gaba da shari'arsa daga Ghana har kotu ta tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar PDP na gaskiya.
Amaechi ya bukaci matasan Najeriya su shiga harkokin siyasa domin samun damar zama gwamnoni, ministoci da sauran shugabanni.
Asali: Legit.ng

