Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Yi Tukin Tasi Domin Rufa Wa Kansa Asiri a Amurka

Tinubu Ya Fadi Yadda Ya Yi Tukin Tasi Domin Rufa Wa Kansa Asiri a Amurka

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya taba tukin tasi da wasu ayyuka a Amurka domin samun kudin biyan kudin karatunsa a jami'a
  • Tinubu ya ce kalubalen da ya fuskanta wajen neman ilimi sun yi tasiri kan manufofin gwamnatinsa na tallafa wa dalibai
  • Shugaban ya ce NELFUND ta raba sama da Naira biliyan 372 ga dalibai, yayin da gwamnati ke gyara makarantun likitanci 24

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya taba tukin tasi da gudanar da wasu ayyuka daban-daban a Amurka domin tara kudin da zai biya karatunsa na jami'a.

Tinubu ya ce kalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake kokarin samun ilimi sun taimaka wajen tsara manufofin gwamnatinsa kan samar da damar karatu ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kwadagon da ya yi a Amurka don biyan kudin makaranta

Tinubu ya yi tukin tasi a Amurka
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yadda Tinubu ya yi tukin tasi

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026, inda ya yi bayani kan matakan da gwamnatinsa ke dauka domin bunkasa harkar ilimi.

A cikin sakon, Tinubu ya ce:

“Lokacin da na fara zuwa Amurka a matsayina na matashi, na rika tukin tasi domin samun kudin karatuna. Har na dage fara karatu na tsawon watanni saboda tara isassun kudade.”

Tinubu ya yi bayani kan tallafin NELFUND

Shugaban kasar ya bayyana cewa ilimi na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta sanya a gaba, inda ya yi nuni da Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Kasa (NELFUND) a matsayin daya daga cikin shirye-shiryen da ake amfani da su.

Tinubu ya ce asusun ya riga ya raba sama da Naira biliyan 372 ga dalibai domin biyan kudin makaranta da kuma bukatun rayuwarsu a manyan makarantun gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya yi ta'aziyyar shugaban karamar hukumar da ya rasu a Bauchi

An kafa asusun ne karkashin dokar ba da lamunin karatu ta shekarar 2024, wadda Tinubu ya sanya wa hannu a watan Afrilun 2024.

Dokar ta cire sharadin samun iyaka kan kudin shigar iyali da kuma bukatar mai tsaya wa dalibi, wadanda a baya suka hana wasu samun damar cin gajiyar shirin.

A tsarin biyan bashin, daliban da suka amfana za su fara mayar da kudin ne bayan shekaru biyu da kammala bautar kasa ta NYSC.

Da zarar sun samu aikin yi, za a rika cire kashi 10 cikin 100 na albashinsu duk wata domin biyan bashin.

Wahalar da Tinubu ya sha a baya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Getty Images

Gwamnati ta gyara kwalejojin fasaha 38

Tinubu ya kuma bayyana cewa shirin gwamnati na koyar da sana'o'in hannu da fasaha ya samu sama da mutane miliyan 2.8 da suka nemi shiga.

Ya ce an gyara kwalejojin fasaha guda 38, yayin da dalibai a kwalejojin gwamnatin tarayya da wasu na jihohi ke samun karatu kyauta.

Ya kara da cewa tallafin ya hada da masauki, litattafai da kayan makaranta, domin rage nauyin da ke kan iyayen dalibai.

Kara karanta wannan

An bude wa Tinubu dakin Ka'aba ya shiga, 'yan Najeriya sun yi martani

Kudin da ake kashewa a bangaren likitanci

A bangaren jami'o'i, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ta cimma sabon matsaya da Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Kasa (ASUU), wadda ta kunshi karin albashin malaman jami'o'i da kashi 40 cikin 100.

Ya ce an kuma bullo da matakan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da dorewar harkokin karatu a jami'o'in kasar.

Bugu da kari, Tinubu ya bayyana cewa gwamnati na kashe Naira biliyan 110 wajen gyaran makarantun koyon aikin likitanci guda 24.

A cewarsa, yawan daliban da ake dauka a fannin jinya a kowace shekara ya karu daga 28,000 zuwa 115,000.

Haka kuma, adadin daliban da ke shiga fannin karatun likitanci da aikin hakori ya karu daga 5,000 zuwa 12,000.

Sanusi II ya ba Tinubu shawara

An ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce yawan bashin Najeriya da almubazzarancin kudaden gwamnati na barazana ga dorewar tattalin arzikin kasar.

Sanusi ya bayyana cewa biyan bashin Najeriya ya cinye kashi 124 cikin 100 na kudaden shigar gwamnatin tarayya a farkon shekarar 2026.

Tsohon gwamnan CBN ya bukaci gwamnati ta fifita wutar lantarki, noma, hanyoyi da fasaha wajen kashe kudaden kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.