Sanata Ya Yi Magana kan Saƙon Yan Sanda bayan An Yi Yunkurin Kashe Shi a Wurin Kamfe

Sanata Ya Yi Magana kan Saƙon Yan Sanda bayan An Yi Yunkurin Kashe Shi a Wurin Kamfe

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya ce bai samu takardar gayyata daga rundunar ’yan sandan jihar Delta ba
  • Ya ce harin da aka kai wa gangamin jam’iyyarsa ta NDC ya yi sanadin mutuwar manyan mambobin tawagarsa
  • Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutum shida a harin, yayin da wasu da dama suka jikkata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege, ya musanta zargin ƙin amsa gayyatar ’yan sanda ba kan harin da aka kai wa tawagar yakin neman zabensa.

Tun farko, Legit Hausa ta ruwaito muki yadda yan daba suka kai hari wurin gangamin yaƙin neman zaɓen NDC a ranar Litinin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane a Uduere, Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Arewa a Jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnan Edo na da hannu a harin da aka kai wa su Kwankwaso? An samu bayani

Omo Agege.
Tsohon mataimakin shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege Hoto: Senator Ovie Omo-Agege
Source: Twitter

Omo-Agege ya musanta kin amsa gayyata

Daily Trust ta rahoto cewa Omo-Agege ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mai Ba Shi Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Sunny Areh, ya fitar.

Ya ce bai samu wata takardar gayyata a hukumance daga rundunar ’yan sandan jihar ba, inda ya jaddada cewa sai da ya ji labarin gayyatar ta kafafen yaɗa labarai.

Ya bayyana rahoton da ke cewa ya ƙi amsa gayyatar ’yan sandan a matsayin “ƙarya”.

Sanata Omo-Agege ya ƙara da cewa, “Ba za ka iya ƙin amsa gayyatar da bai iso gare ka ba.”

Ya bayyana cewa babu wata takardar gayyata a hukumance ko wani jami’in ɗan sanda da ya je wurinsa ko ofishinsa domin miƙa masa gayyatar.

Yadda aka yi yunkurin kashe sanatan

Haka kuma, ya yi watsi da zargin cewa ya ƙi ba masu bincike haɗin kai, yana mai cewa zargin ya samo asali ne daga mutum guda da ba a bayyana sunansa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta tabbatar da kashe mutum kusan 100 a jihar

Omo-Agege ya ce shi ne aka yi niyyar kashewa a harin, wanda ya yi sanadin mutuwar manyan mambobin tawagarsa ta yaƙin neman zaɓe.

Ya ce wasu mutane da dama sun samu munanan raunuka kuma har yanzu suna kwance a asibiti, inda ya buƙaci a gano waɗanda suka aikata harin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Omo-Agage ya ja hankalin yan sanda

Ya tabbatar da cewa zai amsa duk wata sahihiyar gayyatar ’yan sanda da ta dace da doka “da zarar an miƙa masa ita a hukumance” ta ofishinsa.

IGP Disu.
Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, IGP Gunji Disu a ofis a Abuja Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Ya kuma buƙaci ’yan sanda su bi ƙa’idojin da doka ta tanada, yana mai cewa bai dace a sanar da jama’a cewa an gayyaci mutum ba kafin a miƙa masa takardar gayyatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa,

“Sanar da gayyata ta kafafen yaɗa labarai kafin ta isa ga wanda aka ambata ba bin ƙa’ida ba ne, kuma ba zan amince a yi mini shari’a a kafafen yaɗa labarai ba.”

Kotu ta soke takarar Sanata Omo-Agege

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Warri a Jihar Delta ta soke takarar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.

Kotun ta umarci INEC da ta cire sunansa daga cikin jerin ’yan takarar zaɓen 2027, tare da hana shi bayyana kansa a matsayin ɗan takarar sanatan Delta ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262