An Gurfanar da Matar da ake Zargi da Wawure Miliyoyin Naira na Mahajjata
- Hukumar EFCC ta gurfanar da wata mata mai suna Hauwa Mohammed Abdulkadir bisa zargin damfarar maniyyatan aikin hajji kuɗi har Naira miliyan 62.5
- Rahotanni sun nuna cewa ana zargin matar da karɓar kuɗin maniyyata bisa alkawarin samar musu da bizar Saudiyya da tikitin jirgin sama
- Kotun ta bayar da belinta kan Naira miliyan 5 tare da wasu sharuda, sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 3 ga Disambar shekarar 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kwara – Hukumar EFCC ta gurfanar da wata mata mai suna Hauwa Mohammed Abdulkadir a gaban Babbar Kotun Jihar Kwara bisa zargin damfarar maniyyatan aikin hajji kuɗi Naira miliyan 62.5.
An gurfanar da matar ne a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026, a gaban Mai Shari’a Haleema Saleeman bisa tuhume-tuhume guda bakwai da suka shafi karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da matar ne a wani sako da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na X bayan gurfanar da Hauwa.
Ana zargin ta damfari maniyyata
EFCC ta ce ana zargin Hauwa Abdulkadir ta gabatar da kanta a matsayin jami’ar kula da takardun tafiye-tafiye, inda ta karɓi kuɗi daga hannun maniyyatan aikin hajji bisa cewa za ta samar musu da bizar shiga Saudiyya da tikitin jirgin sama.
Hukumar ta bayyana cewa zargin ya shafi kuɗin da ta karɓa daga mutane daban-daban tsakanin watan Disamba na 2025 zuwa Afrilu na 2026.
A ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen, EFCC ta ce matar ta karɓi Naira miliyan 39.57 daga hannun Saka Rauf Ajagbe tsakanin Janairu da Fabrairu na 2026.
Ana zargin ta karɓi kuɗin ne bisa alkawarin samar da bizar tafiya Saudiyya domin shi da wasu mutanen da yake wakilta su gudanar da aikin hajji.
Haka kuma, hukumar ta zarge ta da karɓar Naira miliyan 14.705 daga hannun Abdulmehumeen Abdulsalam tsakanin Disamba 2025 da Afrilu 2026 bisa irin wannan alkawari.
Matar ta musanta tuhume-tuhumen
Rahoton Premium Times ya nuna cewa bayan karanta tuhume-tuhumen guda bakwai da ake yi mata, Hauwa Abdulkadir ta musanta aikata laifukan.
Lauyar EFCC, Rashidat Alao, ta bukaci kotu ta sanya ranar fara shari’ar tare da bayar da umarnin tsare wadda ake zargin a gidan yari har zuwa lokacin da za a fara sauraron shari’ar.
Sai dai lauyan wadda ake tuhuma, O. A. Teni, ya nemi kotu ta bayar da belinta domin ta samu damar neman kuɗin da za ta biya domin mayar wa waɗanda take zargin ta damfara kuɗinsu.

Source: Getty Images
Mai Shari’a Haleema Saleeman ta amince da bukatar bayar da belin Abdulkadir kan kuɗi Naira miliyan 5. Kotun ta kuma buƙaci masu tsaya mata uku da kowannensu zai bayar da jinginar kuɗi Naira miliyan 5.
Najeriya ta yi zama da Saudi
A wani labarin, kun ji cewa Najeriya da ƙasar Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2027 cikin lumana.
Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, da Mataimakin Ministan Aikin Hajji na Saudiyya, Dr Abdulfattah Mashat, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a birnin Jeddah.
Yarjejeniyar ta ƙunshi batutuwan kason alhazai da za a bai wa Najeriya, masauki, sufuri, kiwon lafiya da kuma bin dokokin ƙasar Saudiyya.
Asali: Legit.ng


