Matsalar da Tinubu Ya Fara Cin Karo Da Ita bayan Dawowa Najeriya daga Umrah

Matsalar da Tinubu Ya Fara Cin Karo Da Ita bayan Dawowa Najeriya daga Umrah

  • Tsohon gwamnan Osun, Olagunsoye Oyinlola, ya janye goyon bayan da ya bai wa Tinubu domin sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Oyinlola ya ce yarjejeniyar siyasar da ta sa ya goyi bayan Tinubu ta ƙare, saboda ba a cimma burin da ake son cimmawa ba
  • Tsohon gwamnan ya buƙaci Tinubu da Atiku Abubakar su yi ritaya daga siyasa, su bar matasa su karɓi ragamar mulkin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, ya janye goyon bayan da ya bai wa Shugaba Bola Tinubu domin sake zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Oyinlola ya bayyana cewa yarjejeniyar siyasar da ta sa ya goyi bayan Tinubu ta ƙare, yana mai cewa ba su cimma nasarar da suke fata ba.

Kara karanta wannan

Yadda Obasanjo ya yi kutun kutun domin hana Amaechi zama gwamnan Rivers

Tsohon gwamna ya janye goyon bayansa ga Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya a yayin taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Ɗan siyasar na jam’iyyar PDP ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Laraba, cewar PM News.

Tsohon gwamna ya yi watsi da Tinubu

Da aka tambaye shi ko har yanzu yana goyon bayan sake zaɓen Tinubu, Oyinlola ya amsa da cewa:

“Lokacinsa ya ƙare.”

A ranar 20 ga Yuli, 2025, Oyinlola na cikin jagororin PDP a Osun da suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu domin ya sake yin wa’adi na biyu.

Sai dai tsohon gwamnan ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne domin ganin gwamnatin tarayya ta shiga tsakani kan rikicin ƙananan hukumomin jihar Osun.

Ya ce takaddamar da ake yi kan ikon gudanar da ƙananan hukumomi da kuma dakatar da kuɗaɗen da ya kamata su samu ta sa suka nemi hanyar warware matsalar.

Oyinlola ya bayyana cewa goyon bayan da suka bai wa Bola Tinubu dabara ce ta siyasa, ba wai cikakken amincewa da shugabancinsa ba.

Kara karanta wannan

APC ta yi wa Gwamna ƙarfa ƙarfa, ta cire shi a cikin kwamitin kamfen Tinubu

Ya ce dabarar ba ta haifar da sakamakon da suke fata ba, don haka ya janye daga yarjejeniyar jim kaɗan bayan haka.

“Ba mu cimma komai ba."

In ji shi.

Tsohon gwamna ya fadi dalilin jefar da Tinubu
Tsohon gwamnan Osun a Najeriya, Olagunsoye Oyinlola. Hoto: Olagunsoye Oyinlola.
Source: Facebook

Oyinlola ya bukaci Tinubu da Atiku su yi ritaya

Da yake magana kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027, Oyinlola ya buƙaci Tinubu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, su yi ritaya daga siyasa.

Ya bayyana cewa ya kamata a bai wa matasa damar karɓar ragamar shugabancin Najeriya, yana mai cewa shekaru na daga cikin abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su wajen tantance masu neman muƙaman gwamnati.

Tsohon gwamnan ya kuma tuna cewa a baya ya taɓa ba da shawarar sanya iyakar shekarun waɗanda za su iya neman kujerar gwamna.

A halin yanzu, Oyinlola ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, wanda ke neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Wannan matsaya tasa na nufin ya sauya ra’ayin siyasar da ya bayyana tare da sauran jiga-jigan PDP na Osun wajen goyon bayan Tinubu a bara, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Tinubu ya yi tukin tasi a Amurka

Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya taba tukin tasi da wasu ayyuka a Amurka domin samun kudin biyan kudin karatunsa a jami'a.

Tinubu ya ce kalubalen da ya fuskanta wajen neman ilimi sun yi tasiri kan manufofin gwamnatinsa na tallafa wa dalibai.

Shugaban ya ce NELFUND ta raba sama da Naira biliyan 372 ga dalibai, yayin da gwamnati ke gyara makarantun likitanci 24.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.