Yahaya Bello Ya Tsallake Kogi zuwa Kano, Yana Neman Kuri’u Miliyan 2 ga Tinubu
- Dan majalisar tarayya Leke Abejide da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, sun bukaci mazauna Kano su samar wa Tinubu kuri’u
- Sun yi wannan kira ne yayin wani shirin wayar da kan al’ummar Yarbawa da tallafa musu da aka gudanar a Kano
- Yahaya Bello ya ce kuri’u kusan 500,000 da Tinubu ya samu a Kano a 2023 ba su wadatar ba, don haka ake bukatar karin goyon baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan majalisar wakilai ta tarayya, Leke Abejide, da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, sun nemi alfarmar kuri'u ga Bola Tinubu.
Yan siyasar sun bukaci mazauna Kano su samar wa shugaban kasa Bola Tinubu kuri’u miliyan biyu a zaben 2027.

Source: Facebook
Yahaya Bello sun nema wa Tinubu alfarma
Abejide da Bello sun nemi goyon bayan shugaban kasar ne a ranar Asabar, yayin wani shirin wayar da kan al’ummar Yarbawa da tallafa musu da aka gudanar a Kano, cewar Tribune.
Abejide ne ya shirya taron, wanda ke wakiltar mazabun Yagba ta Yamma, Yagba ta Gabas da Mopamuro a majalisar wakilai ta tarayya.
Dan majalisar ya ce gidauniyarsa ta gudanar da shirin tallafa wa jama’a a Kano ne saboda dadaddiyar alakar da yake da ita da mazauna jihar.
Abejide ya nemi goyon bayan Tinubu
Abejide ya bayyana cewa shirin tallafin zai taimaka wa mata masu sana’o’i, musamman wadanda ke fuskantar matsalar karbar bashi daga cibiyoyin hada-hadar kudi.
Ya ce:
“Lokacin da matanmu ke zuwa cibiyoyin hada-hadar kudi suna karbar bashi da kudin ruwa da ba za su iya biya ba, ya kare har abada. Muddin ke mace ce mai sana’a kuma kina zaune a Kano, lokacin da za ki samu sauki ya zo, da yardar Allah.
“Ban zo nan kawai domin kashe kudin da na yi wahala na samu ba, ina kuma neman goyon bayanku ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.”

Source: Facebook
Yahaya Bello ya ce kuri’u 500,000 sun yi kadan
A nasa bangaren, Yahaya Bello ya bayyana cewa kuri’u kusan 500,000 da Tinubu ya samu a Kano a zaben shugaban kasa na 2023 ba su gamsar da shi ba.
Tsohon gwamnan ya ce:
“Yawan masu kada kuri’a a Kano ya samar wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kuri’u kusan 500,000 a zaben shugaban kasa da ya gabata. Wannan sakamako bai gamsar ba, kuma dole ne mu kara kokari a wannan karon.”
Ya ce yana da yakinin cewa ya kamata kuri’un da jihar za ta samar wa shugaban kasar su kai miliyan biyu ko fiye da haka.
Bello ya kuma bukaci a tabbatar da cewa goyon bayan bai tsaya ga zaben shugaban kasa kadai ba, har da sauran ‘yan takarar APC a dukkan matakan zabe.
Gwamnan Kano ya yabawa shirin tallafin
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba da shirin tallafa wa jama’a da Abejide ya gudanar, yana mai cewa Kano gida ce ga dukkan wadanda ke da alaka da jihar.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare hakkokin mazauna jihar, tabbatar da zaman lafiya da kuma samar musu da damar shiga harkokin tattalin arziki da siyasa.
Ya ce ko da yaushe kofar gwamnatinsa a bude take, kuma za ta tabbatar da cewa kowa ya samu damar bayar da gudunmawa wajen ci gaban Kano.
Za a nema wa Tinubu kuri'u a Arewa
A baya, an ji cewa dan majalisar wakilai, Hon. Leke Abejide ya bukaci hadin kan Yarbawa a yankin kan zaben 2027.
Hon. Abejide ya bukaci shugabannin Yarbawa a Arewa su marawa Bola Tinubu baya a takararsa ta 2027 don ci gaban al'umma.
A taron cika shekara 10 na shugabannin gargajiya na Yarbawa a Arewa, Abejide ya jaddada muhimmancin hadin kai da gujewa siyasar rarrabuwar kawuna.
Asali: Legit.ng


