Attajirin da babu kamarsa a Afrika, Dangote Ya Yi Bayanin Sirrin Nasararsa a Rayuwa

Attajirin da babu kamarsa a Afrika, Dangote Ya Yi Bayanin Sirrin Nasararsa a Rayuwa

  • Alhaji Aliko Dangote, ya ce sirrin nasararsa a rayuwa shi ne taimakon mabukata, abin da ya koya daga wajen mahaifiyarsa
  • Ya bayyana cewa mahaifiyarsa ta kasance tana ciyar da kusan mutane 12,000 abinci sau uku a rana na tsawon shekara
  • Dangote ya ce yana son 'ya'yansa su gaji wannan dabi'a, kuma ya yi wasiyyar sadaka da kashi daya bisa uku na dukiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Industries Limited, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana silar nasararsa har ya yi nisa yau a rayuwa.

Aliko Dangote yake cewa taimakon jama'a da bayar da sadaka shi ne babban sirrin nasararsa a rayuwa, ya ce wajen mahaifiyarsa ya koyi wannan.

Aliko Dangote
Aliko Dangote tare da diyarsa da wasu ma'aikatan kamfaninsa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Aliko Dangote ya halarci taron kungiyar WIMBIZ

Vanguard ta ce Dangote ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi wajen wata tattaunawa kan damammakin da ke Afrika.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya fasa kwai, ya tona abin da ya sa Kwankwaso yake tare da Peter Obi

An gudanar da taron ne a bikin cika shekaru 25 da kafa kungiyar WIMBIZ ta mata masu harkokin kasuwanci, jagoranci da kuma ayyukan gwamnati.

Tattaunawar, wadda Rolake Akinkugbe Filani, shugabar kamfanin EnergyInc Advisors, ta jagoranta a Legas ta samu halartar mata kusan 2,000.

Mahaifiyar Aliko Dangote ta koya masa taimakon jama'a

An tambaye shi irin darussan da ya koya daga matan gidansu, musamman mahaifiyarsa da sauran danginsa da suka yi fice a wajen harkokin kasuwanci.

Attajirin na nahiyar Afrika ya ce babban abin da ya koya shi ne taimakon mabukata da marasa karfi.

Ya ce:

"Daga mahaifiyata na koyi yadda ake taimakon jama'a. A koyaushe tana magana kan taimakon mabukata.
A shekarun 1980s, tana tabbatar da cewa a kowace rana ana ciyar da kusan mutane 12,000 abinci sau uku a rana, sannan ana raba sinkin burodi kusan 35,000 a kullum."

Dangote yana shirin raba miliyoyi da yunwa

Kara karanta wannan

Bangare 1 da Bola Tinubu ya yi wa Atiku da Peter Obi fintinkau a siyasa

Alhaji Dangote mai shekara 69 ya ce a halin yanzu akwai bukatar taimaka wa mutane da dama saboda karuwar masu fama da matsin rayuwa.

Ya bayyana cewa suna nazarin hanyoyin kai dauki ga mafi raunin al'umma, inda suke da burin taimaka wa mutane miliyan 100 a shekara da abinci.

"A yanzu akwai mutane da dama da ke bukatar taimako. Ba na son bayyana komai a nan, amma muna duba yiwuwar isa ga mafi yawan wadanda ke cikin mawuyacin hali domin ganin irin taimakon da za mu iya yi.
"Burinmu shi ne ciyar da mutane miliyan 100 a kowace shekara."

- Aliko Dangote

Mai kudin Afrika ya yi wasiyya da dukiyarsa

A wurin taron, babban attajirin ya sake nanata cewa yana kokarin tabbatar da cewa 'ya'yansa sun gaji dabi'ar taimakon jama'a daga gare shi.

Ya ce a matsayinsa na Musulmi, yana da damar ware kashi daya bisa uku na dukiyarsa domin ayyukan alheri da sadaka bayan ya cika.

‘Dan kasuwar ya ce ya riga ya rubuta wasiyya a hukumance tare saboda gudun a samu sabani game da dukiyarsa bayan rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

'Ƙwarewar da ɗana ke da ita na zama gwamna': Sule Lamido ya magantu

Dangote
Aliko Dangote tare da Devakumar Edwin da Halima Dangote Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tarihin Mariya Sunusi Dantata

Kuna da labari cewa Hajiya Mariya Sunusi Dantata, mahaifiyar Aliko Dangote, ta shahara wajen taimakon marayu da masu karamin karfi.

Ana hasashen cewa tsohuwar mai shekaru fiye da 80 tana ciyar da mutane sama da 50,000 kullum a gidanta da ke Kano.

Ta mayar da gidanta mafakar marasa galihu, inda take ba su abinci da sauran tallafi kamar daukar dawainiyar tarin masara lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng