Shugaban Kasa Ya Yi Murabus saboda Gaza Shawo kan Matsalolin Jama'ar Shi

Shugaban Kasa Ya Yi Murabus saboda Gaza Shawo kan Matsalolin Jama'ar Shi

  • Shugaban ƙasar Paraguay, Santiago Peña, ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa bayan wani babban banki ya faɗa cikin matsalar kuɗi
  • Lamarin ya jawo rikicin siyasa, inda ’yan majalisar dokokin ƙasar suka zargi shugaban da saɓa ƙa’idojin gudanar da aiki
  • Murabus ɗin nasa ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin ƙasar ke shirin gudanar da zaman tsige shi daga kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Asunción, Paraguay – Shugaban ƙasar Paraguay, Santiago Peña, ya sanar da yin murabus bayan rushewar wani banki da ya jawo masa matsala ta siyasa.

Peña ya bayyana matakin nasa ne a cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya nemi afuwar al’ummar ƙasar idan ya taɓa kasa sauke nauyin da aka ɗora masa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Santiago Peña
Shugaban Paraguay, Santiago Peña. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton BBC ya nuna cewa shugaban ya ce bai taɓa da niyyar cin amanar amincewar da jama’a suka ba shi ba.

Rikicin ya ƙara kamari ne bayan bankin Ueno ya shiga tsarin fatarar kuɗi, wanda ya sa aka dakatar da dukkan ayyukansa.

Rushewar bankin Ueno ta jawo rikici

Bankin Ueno, wanda ya ce yana da kwastomomi kusan miliyan 3, ya shiga matsalar kuɗi a farkon makon nan, lamarin da ya hana miliyoyin mutane samun damar shiga asusunsu.

Bankin na kula da asusun fansho da wasu kuɗin gwamnati, wanda ya ƙara tsananta damuwar jama’a bayan dakatar da ayyukansa.

Babban bankin ƙasar Paraguay ya karɓe ikon kula da bankin, yayin da mutane suka fito zanga-zanga suna neman shugaban ƙasar ya sauka daga muƙaminsa.

Hukumomi sun naɗa sabon shugaban babban bankin ƙasar, sannan majalisar dokoki ta amince da wani tsari na biyan mutanen da suka ajiye kuɗin a bankin.

Kara karanta wannan

"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027

An zargi Peña da saɓa ƙa’idoji

’Yan majalisar dokokin Paraguay sun zargi Peña da samun saɓanin muradun kai da na gwamnati, saboda a baya ya kasance mai hannun jari a kamfanin da ya mallaki bankin.

Shugaban ya riƙe hannun jarin kamfanin har zuwa shekarar da ta gabata, abin da ya sa wasu ’yan majalisa ke zargin cewa alaƙarsa da bankin ta haifar da rashin gaskiya wajen gudanar da mulki.

Sai dai rahoton da CNN ta walllafa ya bayyana cewa Peña ya ƙaryata zargin aikata ba daidai ba.

Santiago Peña a taron UN
Shugaban kasar Paraguay a taron majalisar dinkin duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Majalisar wakilai ta ƙasar ta kaɗa ƙuri’ar goyon bayan ci gaba da shirin gurfanar da shi domin tsige shi daga muƙaminsa.

Haka kuma, hotunan da aka ɗauka a kusa da ginin majalisar dokokin ƙasar a ranar Alhamis sun nuna arangamar jami’an tsaro da masu zanga-zanga da ke neman a cire shugaban daga mulki.

APM ta nemi Tinubu ya janye takara

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APM ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya janye daga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 tare da marawa ɗan takararta, Seyi Makinde, baya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Abubakar Yusuf, ya fitar, APM ta ce Tinubu ya gaza nuna ƙwarewar jagoranci da Najeriya ke buƙata.

Yusuf ya yi zargin cewa Tinubu ya bar gudanar da wasu muhimman ayyukan ofishinsa a hannun wasu mutane da ba zaɓaɓɓu ba, ciki har da ’yan uwansa da hadimansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng