Obi Ya Shiga wa Atiku Fada kan Rusa 'Yan Takarar ADC da Kotu Ta Yi
- Peter Obi ya nuna damuwa kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta soke zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027
- Obi ya ce hukuncin na iya jawo rashin tabbas ga jam’iyyun adawa gabanin zaɓe, tare da shafar damar masu zaɓe wajen zaɓar shugabannin da suke so
- Tsohon gwamnan Anambra ya kuma zargi jam’iyyar mai mulki da amfani da dabarun siyasa wajen raunana jam’iyyun adawa da hana su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya nuna damuwa kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na soke zaɓen Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar ADC a 2027.

Kara karanta wannan
"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027
Obi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, inda ya ce hukuncin na iya haifar da rashin tabbas ga jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen ƙasar.

Source: UGC
Puch ta wallafa cewa hukuncin da Mai shari’a Peter Lifu ya yanke ya kuma soke shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark da matakan da ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Hukuncin ya ba Obi mamaki
Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce ya samu labarin hukuncin ne cikin mamaki, yana mai bayyana shi a matsayin abin da ya tayar masa da hankali.
Obi ya jaddada cewa ba ya ƙalubalantar ikon kotu na yanke hukunci kan rikice-rikicen shari’a, amma ya ce yana damuwa da rashin tabbas da hakan zai iya haifarwa a siyasar ƙasar.
Ya bayyana cewa bai dace a samu ruɗani kan ’yan takara da jam’iyyun siyasa makonni kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa ba.
A cewarsa, yana da matuƙar muhimmanci a samu tabbataccen yanayi domin masu zaɓe su san waɗanda za su zaɓa.
Obi ya zargi APC da raunana adawa
A sakon da ya wallafa a X, Peter Obi ya yi zargin cewa jam’iyyar mai mulki ce ke haddasa rashin kwanciyar hankalin da ake samu a wasu jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan
Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya
Ya danganta hakan da rikicin da ya dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsa ta LP, yana mai cewa ana amfani da irin waɗannan dabaru wajen takura wa ’yan adawa da hana su gudanar da kamfen.
Obi ya ce ɗaya daga cikin ginshiƙan dimokuraɗiyya shi ne bai kamata kotu ta zama ita ke zaɓar shugabanni a madadin jama’a ba, domin masu zaɓe ne ya kamata su yanke wannan matsaya.

Source: Facebook
Sai dai ya jaddada cewa yana da cikakken amincewa da bangaren shari’a, yana mai cewa ya nuna girmamawa ga kotuna a lokacin da yake riƙe da muƙaman gwamnati.
Atiku ya yi magana
A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya zargi wasu mutane da ƙulla makircin siyasa da amfani da hukuncin kotu wajen raunana jam’iyyar ADC da kawo cikas ga takararsa.
Atiku ya ce hukuncin kotun ya zo ne kwana guda bayan dimbin magoya bayansa sun fito tarbarsa a Sokoto yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga magoya bayan ADC da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da yaɗa saƙon jam’iyyar cikin lumana.
Asali: Legit.ng