Atiku Ya Hango Matsala, Ya Bukaci Mutane Su Fito Su Yi Zabe kamar Ranar Tashin Alkiyama

Atiku Ya Hango Matsala, Ya Bukaci Mutane Su Fito Su Yi Zabe kamar Ranar Tashin Alkiyama

  • Atiku Abubakar ya zargi wasu ’yan APC da zagayawa ƙauyukan Arewacin Najeriya suna sayen katunan zaɓe domin yin maguɗi
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan Najeriya su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu, su kada kuri’a tare da kare ta
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce an zaɓi Sokoto domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne saboda muhimmancinta a tarihi da addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya zargi wasu mambobin APC da zagaya ƙauyukan Arewacin Najeriya suna sayen katunan zaɓe da nufin yin maguɗi a zaɓe.

Atiku ya yi wannan zargi ne a ranar Laraba a Sokoto, lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC.

Kara karanta wannan

Yadda Dogo Gide ya zama alaƙaƙai ga kungiyar IS a Arewacin Najeriya

Atiku.
Atiku, Abubakar, Rotimi Amaechi, Sanata Aminu Waziri Tambuwal a wurin kaddamar da yakin neman zaben ADC a Sokoto Hoto: Rt. Hon. Chibuike R. Amaechi
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, jagoran yan adawa ya buƙaci ’yan Najeriya su fito da yawa domin kaɗa ƙuri’a tare da kare ƙuri’unsu kamar ranar tashin alƙiyama.

Atiku da tawagarsa sun isa Sokoto da misalin ƙarfe 1:00 na rana, amma ba su isa inda aka shirya gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen ba, sai da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, sakamakon dimbin jama’ar da suka fito domin tarbarsu.

Atiku ya bukaci mutane su fito zabe

Ya yi gargaɗin cewa rashin fitowa zabe zai iya ba wa waɗanda ake zargin suna sayen katunan zaɓe damar yin maguɗi, tare da ƙoƙarin nuna cewa jam’iyyun adawa ba su da isassun magoya baya a Arewa.

“Mu fito mu kaɗa ƙuri’a kamar ranar tashin alkiyama ce. Mu fito da yawa, mu kare ƙuri’unmu, sannan mu raka su har sai an tabbatar da tsaronsu.
“Idan ba ku fito ba, wasu za su riƙa zagayawa ƙauye-ƙauye suna sayen katunan zaɓe domin su nuna cewa ba mu da magoya baya da yawa kamar waɗanda ke Kudu. Ku fita ku kaɗa ƙuri’unku, sannan ku kare su,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku ya kaddamar da kamfen a Sokoto, ya yi muhimman alkawura ga 'yan Najeriya

Dalilin kaddamar da kamfe a Sokoto

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce an zaɓi Sokoto domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne saboda muhimmancinta a tarihi da addini, yana mai bayyana jihar a matsayin cibiyar zaman lafiya da zaman tare a Najeriya.

“Sun ce ba za mu zo Sokoto ba, amma ga mu nan. Sun ce ba za mu gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe ba, amma mun zo.
“Ina bin tarihi, sannan na yi imani da zaman tare cikin lumana. Sokoto cibiyar zaman lafiya ce, kuma mabiya dukkan addinai sun fahimci muhimmancin Sokoto ga Najeriya. Wannan ne ya sa muka yanke shawarar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenmu a Sokoto,” in ji shi.
ADC .
Magoya bayan ADC a wurin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a Sakkwato Hoto: Rt. Hon. Chubuike Rotimi Amaechi
Source: Facebook

An rika rera 'Tinubu must go' a Sokoto

Kun ji cewa magoya bayan ADC sun riƙa rera taken “Tinubu Must Go” yayin ƙaddamar da yakin neman zaben dan shugaban ƙasa na jam’iyyar a Sakkwato.

Masu halartar gangamin sun bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar tare da nuna rashin gamsuwarsu da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262