Gwamna Ya Yi Magana Mai Zafi kan Harin da Aka Kai Wa Ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Gwamna Ya Yi Magana Mai Zafi kan Harin da Aka Kai Wa Ayarin Peter Obi da Kwankwaso

  • Gwamna Bassey Otu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC a Calabar
  • Ya umurci jami’an tsaro su gano tare da kama waɗanda suka aikata harin domin gurfanar da su a gaban shari’a
  • Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali ko aikata laifuka a harkokin siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River, Nigeria - Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Bassey Otu, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso a Calabar.

Gwamna Otu ya umarci jami’an tsaro su gano waɗanda suka aikata harin kuma su kama su domin su girbi abin da suka shuka.

Gwamna Otu.
Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu yana jawabi a wurin taro Hoto:Bassey Otu
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaransa, Mista Linus Obogo, ya fitar.

Kara karanta wannan

"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027

Gwamna ya jajanta wa Peter Obi

Bassey Otu ya bayyana alhininsa kan lamarin da ya faru ranar Laraba yayin ziyarar yaƙin neman zaɓen Peter Obi da Kwankwaso a babban birnin jihar.

“Ina miƙa saƙon jaje da ya fito daga zuciyata ga Mista Peter Obi da tawagarsa bisa mummunan lamarin da ya faru jiya yayin ziyarar yaƙin neman zaɓensa a babban birnin jiharmu,” in ji Otu.

Gwamnan ya ce Jihar Cross River na tare da dukkan ’yan siyasa da ke neman yin hulɗa da masu zaɓe cikin lumana, yana mai jaddada cewa bai kamata a tsoratar da kowa ko hana shi amfani da haƙƙinsa na siyasa ba.

Ya bayyana harin a matsayin abin da ya saɓa wa martabar jihar ta fuskar karɓar baƙi da zaman lafiya, yana mai cewa lamarin bai nuna kyawawan ɗabi’un al’ummar Cross River ba.

Gwamna ya yi gargaɗi kan tashin hankali

“An daɗe ana alfahari da Jihar Cross River a matsayin cibiyar karɓar baƙi, karamci da kyawawan ɗabi’u a Najeriya. Al’adunmu sun ginu ne kan zaman lafiya, jituwa da mutunta juna, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyar siyasa ba,” in ji shi.

Kara karanta wannan

"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"

Otu ya ce harin abin Allah-wadai ne kuma ba abin amincewa ba ne, yana mai tabbatar wa jam’iyyun siyasa cewa jihar a shirye take ga dukkan harkokin siyasa da suka dace da doka kuma ake gudanarwa cikin lumana.

Obi da Kwankwaso.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi tare da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Ya gargaɗi cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali a harkokin siyasa ko aikata laifuka ta kowace hanya ba.

Yadda aka farmaki ayarin Peter Obi

Kun ji cewa an kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, hari a Calabar, jihar Cross River.

An ce maharan sun jefi ayarin motocin da duwatsu da wasu abubuwa, lamarin da ya haddasa lalacewar wasu motocin da ke cikin ayarin.

Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun dakile yiwuwar barkewar rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da na NDC a Calabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262