Kotu Ta Soke Tikitin Dan Takarar Gwamna a 2027, Ta Umarci a Sake Zaben Fitar da Gwani

Kotu Ta Soke Tikitin Dan Takarar Gwamna a 2027, Ta Umarci a Sake Zaben Fitar da Gwani

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke zaben fitar da gwanin jam'iyyar ADC na takarar gwamnan jihar Nasawara
  • Mai Shari’a Garba Umar ya umurci jam’iyyar ta sake gudanar da zaben fitar da gwani a rumfunan zabe 11 na Karamar Hukumar Karu
  • Kotun ta hana Angbazo gabatar da kansa a matsayin dan takarar ADC, sannan ta hana INEC amincewa da takararsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Mai Shari’a Garba Umar, ta soke takarar Manjo Janar Nuhu Angbazo (mai ritaya) a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar ADC.

Kotun ta kuma umarci jam’iyyar ADC da ta sake gudanar da sabon zaben fitar da gwani a Karamar Hukumar Karu domin tsaida sahihin dan takarar gwamna a Nasarawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya yi ta'aziyyar shugaban karamar hukumar da ya rasu a Bauchi

ADC .
Tambarin jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya Hoto Bolaji ADC
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa a hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Umar ya kuma hana Angbazo gabatar da kansa a matsayin dan takarar ADC a zaben gwamnan jihar na 2027.

Kotu ta bai wa INEC umarni

Haka kuma, kotun ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) amincewa da shi a matsayin dan takarar jam’iyyar ADC.

Tsohon Ministan Muhalli, Mohammed Hassan Abdullahi, ne ya shigar da karar. Shi ma ya tsaya takarar gwamna a zaben fitar da gwani na ADC tare da Angbazo da Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Kudu, Mohammed Ogoshi Onawo.

Kotun ta bayyana cewa zaben da ya samar da Angbazo bai kammala ba, saboda ba a hada sakamakon zaben Karamar Hukumar Karu cikin sakamakon da aka sanar ba.

Dalilin soke zaben fitar da gwani

Da yake karin haske kan hukuncin, kotun ta ce umarnin da ta bayar a bayyane yake: an soke Angbazo a matsayin dan takarar ADC, kuma an hana shi gabatar da kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna na 2027.

Kara karanta wannan

Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano

Kotun ta kuma bayyana cewa zaben fitar da gwani bai kammala ba, domin sakamakon Karu bai cikin sakamakon da aka sanar, kamar yadda Punch ta kawo.

A cewar kotun, wadanda ake kara sun amince cewa ba a gudanar da zabe a Karu ba. Saboda haka, ba za a iya daukar zaben a matsayin wanda aka kammala ba, kuma dole ne a gudanar da zabe a karamar hukumar kafin jam’iyyar ta samu sahihin dan takara.

Nuhu Angbazo.
Dan takarar gwamnan jihar Nasarawa karkashin inuwar ADC, Nuhu Angbazo Hoto: Major General Nuhu Angbazo
Source: Facebook

Hukuncin ya umurci jam'iyyar ADC da ta sake gudanar da zabe a dukkan mazabu 11 na Karamar Hukumar Karu kafin ta iya tsayar da dan takara bisa ka’ida.

Kotun ta sake jaddada cewa ta hana INEC amincewa da Angbazo a matsayin dan takarar ADC, yayin da ita ma ta hana Angbazo gabatar da kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Kotu ta soke zaben APC a Gombe

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zama Gombe ta soke zaben fitar da gwanin APC na takarar Majalisar wakilai a mazabar Balanga/Billiri.

A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Vera E. Ibrahim ta umarci APC ta gudanar da sabon zabe a wannan mazaba tare da hana Ali J.C. sake tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262