Umarnin da APC Ta Ba Ministoci da Masu Mukamai kan Kamfen Tinubu a 2027
- Jam’iyyar APC ta umarci ministoci da masu mukaman siyasa su halarci gangamin yakin neman zaben Tinubu a jihohinsu kawai
- Umarni na kunshe ne cikin wata takardar da darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa
- Jam’iyyar ta bukaci jami’anta su mayar da hankali wajen wayar da kan magoya baya daga rumfunan zabe zuwa kananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC ta ba da umarni ga ministoci, masu rike da mukaman siyasa da mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa.
Jam'iyyar APC ta bukace su da su halarci gangamin yakin neman zabe da aka shirya a jihohinsu kawai gabanin zaben 2027.

Source: Twitter
An bayyana hakan ne cikin wata takardar umarni da Abdulaziz Yari, darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC (PCC), ya sanya wa hannu, cewar TheCable.
A cewar takardar, manufar gangamin ita ce tattara magoya bayan APC da kuma sanar da masu zabe irin nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu.
APC ta fayyace aikin ministoci da masu mukamai
Kwamitin yakin neman zaben ya umurci ministoci da sauran masu mukaman siyasa da su mayar da hankali wajen wayar da kan jama'a a rumfunan zabensu, mazabunsu da kananan hukumominsu.
Wannan umarni na cikin tsarin yakin neman zaben da jam’iyyar ta kira da tsarin dala, wanda aka tsara domin gudanar da ayyukan siyasa tun daga matakin kasa har zuwa tushe.
Takardar ta bayyana cewa:
“Ministoci da sauran masu mukaman siyasa dole ne su halarci gangamin da aka shirya a jihohinsu na asali kawai. An yi hakan ne domin tabbatar da ingantaccen tsari da gudanar da ayyukan yakin neman zabe yadda ya kamata.”
Haka kuma, an umurci daraktocin sassan kwamitin da ba su da takamaiman aikin yi a wajen gangamin da su mayar da hankali wajen aiwatar da tsare-tsarensu da kasafin kudaden da aka amince da su.

Source: Twitter
Umarnin da aka ba shugabannin APC na kasa
Dangane da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na APC, Yari ya ce mambobinsa su mayar da hankali kan ayyukan jam’iyya da wayar da kan jama'a a jihohinsu da yankunansu.
Sai dai ya kebance shugaban jam’iyya na kasa, sakataren jam’iyya na kasa, shugabar mata ta kasa, shugaban matasa na kasa da sakataren shirye-shiryen jam’iyya na kasa daga wannan umarni.
Duk da haka, takardar ta ce sauran mambobin kwamitin NWC ana sa ran za su halarci gangamin da aka shirya a jihohinsu na asali, cewar Punch.
APC za ta karfafa yakin neman zabenta
Kwamitin yakin neman zaben ya kuma bayyana cewa zai kara bai wa 'yan takarar APC da ke neman kujerun majalisun dokokin jihohi, majalisar wakilai da majalisar dattawa muhimmanci a lokacin gangamin.
Yari ya bukaci daraktoci da su tabbatar da cewa dukkan jami'an da ke karkashinsu sun samu cikakken bayani kan umarnin tare da bin dukkan tanade-tanadensa.

Kara karanta wannan
Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto
An yi barazana ga masu mukamai
Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da tawagar kungiyar dattawan Arewa (ACF) a fadar shugaban kasa.
Bola Tinubu ya ba su umurnin komawa gida su hada kai wajen duba matsalolin Arewa tare da kuma gaggauta nemo mafita.
Shugaban ya kuma bayyana mataki mai tsauri da gwamnatin sa za ta dauka kan dukkan jami'an sa da suka yi kasa a gwiwa.
Asali: Legit.ng

