Atiku Ya Soki DSS, Ya Fadi Makircin da Aka Shirya domin Hana Shi Gangamin Kamfe a Sokoto
- Tsohon mataimakin shugaban kasa ya zargi shugabannin DSS da daukar mutane domin kawo cikas ga kaddamar da yakin neman zaben ADC a Sokoto
- Atiku ya ce an hana jam’iyyar amfani da wasu wuraren gwamnati tare da hana ta tallafin kayan gudanarwa
- Dan takarar shugaban kasar ya zargi gwamnatin Tinubu da kokarin raunana jam’iyyun adawa da mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi shugabannin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da daukar nauyin wasu masu zanga-zanga domin kawo cikas ga kaddamar da kamfen da zai yi a Sokoto.

Kara karanta wannan
Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC
Atiku ya yi wannan zargi ne a ranar Talata, cikin wata sanarwa da ya fitar gabanin bikin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na ADC, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 4 ga Nuwamba, a Sokoto.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa sa yake jawabi ga manema labarai, Atiku ya ce abin da ke faruwa a Sokoto ya wuce sabanin siyasa na yau da kullum da aka saba gani.
Atiku ya yi zargin ana kulla makirci
Ya bayyana lamarin a matsayin wani shiri na musamman da aka tsara domin kawo cikas ga ADC da kuma hana ’yan Najeriya damar zabar shugabannin da suke so.
Atiku ya ce:
“Na zo gare ku a yau cikin damuwa, amma da cikakken kudurin tsayawa kan gaskiya. Abin da ke faruwa a Sokoto ba adawar siyasa ba ne. Wani shiri ne da aka kitsa domin dakile ADC, hana ta gudanar da yakin neman zabenta da kuma tauye wa ’yan Najeriya ’yancin zabe.”
Zargin hana ADC damar kamfe
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa an hana jam’iyyar amfani da wasu wuraren gwamnati da ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa su samu damar amfani da su.
Ya kuma ce an hana jam’iyyar wasu tallafin kayan aiki da ake bukata wajen gudanar da kamfe, yana mai cewa wadannan matakai an dauke su ne da gangan domin hana ADC samun damar fafatawa da sauran jam’iyyu cikin adalci.
Atiku ya kara da zargin cewa DSS ce ke da hannu wajen tara mutane domin gudanar da zanga-zanga da nufin haddasa rudani.
Zargin da Atiku ke yi wa DSS
“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, bayanan da muke da su sun nuna cewa shugabannin DSS na daukar mutane domin su gudanar da zanga-zanga a Sokoto.
"Manufar ita ce a haddasa rikici, domin bai wa gwamnatin APC ta jihar, wadda ke karkashinta, hujjar sanya dokar hana fita tare da hana kaddamar da yakin neman zabenmu gudana kamar yadda aka tsara.”
- Atiku Abubakar.

Source: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana lamarin a matsayin katsalandan na siyasa da wata hukumar tsaro ke yi, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Atiku ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da mayar da hankali sosai wajen raunana jam’iyyun adawa masu karfi, maimakon magance matsalolin da ke addabar kasar.
Atiku ya yi alkawarin samar da wuta
Kun ji cewa Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Bola Tinubu da kasa cika alkawarin samar wa ’yan Najeriya wutar lantarki mai ɗorewa tun bayan hawansa mulki.
Atiku ya jaddada cewa samar da wutar lantarki mai ɗorewa da ’yan Najeriya za su iya biya zai kasance cikin manyan abubuwan da zai ba fifiko a ƙasa.
Asali: Legit.ng

