Kamar Buhari, Ana Neman Tallafa wa Kamfen Din Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a 2027
- Aisha Yesufu ta bukaci ’yan Najeriya su bayar da gudummawar kuɗi domin tallafa wa kamfen ɗin Peter Obi na zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Ta ce lokaci ya yi da ’yan Najeriya za su ɗauki nauyin yaƙin neman zaɓen, maimakon dogaro da Obi wajen samar da kuɗaɗe
- ’Yar gwagwarmayar ta yi alƙawarin bayyana yadda aka karɓi gudummawar da yadda aka kashe kuɗin domin tabbatar da gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fitacciyar ’yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta buƙaci ’yan Najeriya su bayar da gudummawar kuɗi ga dan takarar shugaban kasa a 2027.
Aisha ta buƙaci tallafin kudin domin tallafa wa kamfen ɗin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, gabanin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Yesufu ta yi wannan kira ne a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, inda ta bukaci magoya bayan Obi su ɗauki nauyin tallafa wa kamfen ɗinsa da kuɗaɗensu.
Ta ce duk wanda yake son ganin an samu sauyi a Najeriya, ya kamata ya bayar da gudummawar duk kuɗin da zai iya domin ganin an cimma wannan buri.
Aisha Yesufu ta tuna da zaɓen 2023
’Yar gwagwarmayar ta bayyana cewa dole ne ’yan Najeriya su kasance cikin waɗanda ke tallafa wa yunƙurin ceto ƙasar ta hanyar bayar da gudummawar kuɗi.
Ta tuna cewa a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi bai yi maraba da karɓar kuɗaɗen da aka tara daga wajen jama’a ba tun farko.
Sai dai ta ce ta ƙarfafa masa gwiwa ya amince da gudummawar domin waɗanda suka bayar da kuɗi su ji suna da hannu a harkokin kamfen ɗin.
Yesufu ta bayyana cewa an gudanar da irin wannan tara kuɗi a shekarar 2023, inda aka bayyana bayanan kuɗaɗen da aka karɓa da kuma yadda aka kashe su, duk da sukar da wasu mutane suka yi.

Kara karanta wannan
Jerin 'yan Najeriya 4 da suka lashe kujeru daban daban a zaɓen Amurka, na 5 na hanya
Ta ƙara da cewa tsarin da Obi yake ɗaukar mafi yawan nauyin kuɗaɗen gudanar da kamfen ɗinsa ba zai ci gaba da aiki ba.
Ta ce:
“Ba zai ƙara yiwuwa haka ba. Dole ne kowannenmu ya bayar da tasa gudummawar gwargwadon ƙarfinsa.”

Source: UGC
An ware gudummawar kamfen da ta jam'iyya
Aisha Yesufu ta kuma bayyana cewa shirin tara kuɗaɗen da take jagoranta ya bambanta da tsarin gudummawar kuɗaɗen jam’iyyar siyasa.
Ta ce za a yi amfani da kuɗaɗen da ake tarawa ta wannan hanya ne wajen tallafa wa ayyukan kamfen ɗin Obi, yayin da jam’iyyar za ta fitar da bayanan asusunta domin masu son tallafa mata kai tsaye.
Ta shawarci ’yan Najeriya masu sha’awar bayar da gudummawa ga jam’iyyar da su jira sai ta sanar da bayanan asusunta a hukumance.
Haka kuma, Yesufu ta yi alƙawarin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen kula da kuɗaɗen, inda ta ce za ta riƙa bayyana duk gudummawar da aka samu da yadda aka kashe ta.
Ta ce ta yi irin wannan bayani kan gudummawar da aka samu a kamfen ɗin 2023, kuma za ta sake yin hakan gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya
A ƙarshe, ta bukaci ’yan Najeriya masu goyon bayan burin siyasar Peter Obi su bayar da gudummawa domin ganin an gudanar da kamfen da kuɗaɗen ’yan ƙasa.
Abin da Obi ya yi a Calabar
An ji cewa Peter Obi ya bayyana cewa ya ki daukar shawarar jami’an tsaronsa ta sauya hanya bayan samun rahoton cewa ana jifan ayarinsa a Calabar.
Yan sanda sun ce sun hana rikici barkewa tsakanin magoya bayan NDC da APC a gaban otal ɗin Metropolitan da ke Calabar.
Dan takarar shugaban kasar na NDC ya yi gargaɗin cewa ba za a bar irin waɗannan abubuwa su sake faruwa a zaɓen 2027 ba.
Asali: Legit.ng
