Tinubu Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Fim Din da Ta Girgiza Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Pete Edochie, inda ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi
- Tinubu ya ce Edochie na cikin waɗanda suka assasa masana’antar Nollywood, kuma gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa Afirka zuwa yadda take a yau
- Shugaban ya tuna da rawar da marigayin ya taka a matsayin Okonkwo a fim ɗin Things Fall Apart, wanda gidan talabijin na NTA ya shirya bisa littafin Chinua Achebe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Najeriya, Pete Edochie, inda ya bayyana cewa mutuwarsa babban rashi ne ga ƙasar da masana’antar shirya fina-finai.
Shugaban ya bayyana Edochie a matsayin ɗaya daga cikin fitattun jaruman Afirka, wanda ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa Nollywood da yaɗa al’adun Afirka ta hanyar fina-finai.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Source: Instagram
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙon ta’aziyyar da ya wallafa a shafin X na mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga.
Tinubu ya yaba wa Edochie
Tinubu ya tuna da rawar da marigayin ya taka a matsayin Okonkwo a shirin talabijin na Things Fall Apart, wanda gidan talabijin na NTA ya shirya bisa littafin marubuci Chinua Achebe a shekarun 1980.
Ya ce Edochie ya kasance jarumi na musamman, mai mutunci da kuma kwarewa wajen jan hankalin masu kallo, inda ya shafe shekaru da dama yana nishaɗantar da iyalai.
Shugaban ya kuma ambaci fina-finan Igodo, Rituals da Lionheart a matsayin wasu daga cikin ayyukan da suka taimaka wajen bunƙasa Nollywood da kuma ƙara saninta a duniya.
Gudummawar marigayin ga al’adu
Tinubu ya ce yadda Edochie ke taka rawar shugabannin gargajiya, iyalai da kuma sauran halayen zamantakewar Afirka ya taimaka wajen nuna al’adun Najeriya ga masu kallo a sassan duniya.

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur
Ya bayyana cewa marigayin ba jarumi kaɗai ba ne, domin ya kuma yi aiki a matsayin mai gudanarwa, mai watsa shirye-shirye da kuma ɗan jarida.
A cewarsa, gudummawar Edochie ga masana’antar fina-finai, al’adun jama’a da tsarin zamantakewa ba za a iya musantawa ba.

Source: Facebook
Shugaban ya bayyana cewa Edochie ya rayu rayuwa mai ma’ana, kuma ayyukan da ya bari za su sa al’umma su ci gaba da tunawa da shi na tsawon lokaci.
An kama mai shiga makabarta
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekaru 30 bisa zargin haƙa kabari a makabartar Machika da ke Ribah.
Wanda ake zargin mai suna Tapro Tareza, mazaunin ƙauyen Changu da ke gundumar Kanya, ana zarginsa da lalata kaburbura tare da cire wasu abubuwa daga gawarwakin mamata.
Rundunar ta ce an kama shi ne bayan matasan yankin sun cafke shi yana haƙa sabon kabari, sannan suka sanar da ’yan sanda.
Asali: Legit.ng